Ramadan: Gwamna Zulum Ya Ware Musulmi da Kiristoci 300,000, Ya Raba Tallafin Azumi

Ramadan: Gwamna Zulum Ya Ware Musulmi da Kiristoci 300,000, Ya Raba Tallafin Azumi

  • Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kaddamar da rabon tallafin azumi ga Musulmai da Kiristoci a fadin jiharsa
  • Babagana Zulum ya bayyana cewa kowane gida daga cikin gidajen da za su amfana da tallafin zai samu buhun shinkafa, gero da sukari
  • Ya kuma gargadi yan kwamitin rabon tallafin da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da rikon amana, kuma su gujewa sanya wadanda ba su cancanta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya fara rabon kayan tallafin azumi ga gidajen Musulmi da Kirista 300,000 masu ƙaramin ƙarfi a ƙananan hukumomi 27 na jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da al'ummar musulmi a Najeriya da wasu kasashen duniya suka dauki azumin farko a watan Ramadan yau Laraba, 18 ga watan Fabrairun 2025.

Kara karanta wannan

Ramadan: Coci ya yi abin alheri, ya raba wa Musulmi, makarantun tsangaya kayan abinci

Gwamna Zulum.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum a wurin kaddamar da rabon kayan tallafin Ramadan Hoto: @daudailiya
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa a wannan shekara ta 2026, azumin watan Ramadan ya zo lokaci guda da ibadar azumin kiristoci.

Abubuwan da za a raba wa talakawa a Borno

Da yake ƙaddamar da rabon tallafin a birnin Maiduguri, Gwamna Zulum ya ce an shirya wannan tallafi ne domin rage radadin matsin tattalin arziki da ke addabar al’umma masu rauni.

Ya lura cewa azumin Ramadan da kuma lokacin azumin Kiristoci sun zo lokaci guda a bana, yana mai jaddada cewa gidajen Kiristoci ma za su amfana da tallafin.

A cewar gwamnan, kowane gida da ya shiga cikin wadanda za su ci gajiyar tallafin zai samu buhun shinkafa guda, buhun gero guda da kilogiram 10 na sukari.

Farfesa Zulum ya ƙara da cewa an ware ƙarin dubban buhunan shinkafa, gero da sukari domin rabawa tsofaffi da karfin su ya kare a sassan jihar Borno.

Gargadi kan sayar da kayan tallafi

Kara karanta wannan

Saudiyya ta sanar da ranar fara azumi bayan ganin watan Ramadan

Bugu da kari, Zulum ya gargadi kwamitin da ke kula da rabon kayan da su tabbatar da gaskiya da adalci a aikin, tare jan kunnensu da su gujewa sayar da kayan ta bayan fage.

A ruwayar The Guardian, Gwamna Zulum ya ce:

“Wadannan kaya ba na sayarwa ba ne. Ba don abokanka ko ’yan uwanka da ba sa buƙata ba ne, na talakawa ne masu karamin karfi.
"Wadanda ake so su amfana da tallafin su ne zawarawa, marayu, ’yan gudun hijira, manomin da da suka yi asara bana, da kuma masu aikin rana da ke fama da wahala.
"Duk wanda aka kama yana karkatar da kayan ko yana siyarwa, zai fuskanci hukunci mai tsanani bisa tanadin doka."
Gwanna Zulum.
Gwamna Babagana Zulum yayin rabon tallafin azumi ga talakawa a Borno Hoto: @daudailiya
Source: Twitter

An rage lokacin aiki saboda Ramadan a Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed, ya tausaya wa ma'aikatan jihar Bauchi yayin da aka fara azumin watan Ramadan na shekarar 2026.

Sanata Bala Mohammed ya amince da rage lokutan tashi daga aiki ga ma'aikatan gwamnatin jihar a duk tsawon lokacin azumin Ramadan na bana, inda za su rika tashi da karfe 3:00 na yamma.

Ya kuma buƙaci ma'aikata da su yi amfani da wannan lokaci mai tsarki wajen gudanar da addu'o'in neman ci gaba, zaman lafiya, da haɗin kai a jihar Bauchi da kuma Najeriya baki ɗaya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262