Bayan Shekara 11, Uba Sani Ya Dawo da Abin da Aka Daina Yi Wa Kiristoci a Kaduna

Bayan Shekara 11, Uba Sani Ya Dawo da Abin da Aka Daina Yi Wa Kiristoci a Kaduna

  • Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Sanata Uba Sani ta farfado da shirin daukar nauyin sauke faralin Kiristoci
  • Matakin dawo da shirin daukar nauyin sauke faralin Kiristocin na zuwa ne bayan gwamnatocin baya sun dakaatar da shi
  • Shugabar ma'aikatan gwamnatin Kaduna, Jimami C. Bako ta yabawa Gwamna Uba Sani kan matakin da ya dauka na dawo da shirin

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani ya dawo da shirin sauke faralin Kiristoci wanda gwamnatin jiha ke ɗaukar nauyi.

Gwamna Uba Sani ya dawo da daukar nauyin sauke faralin ne bayan dakatar da shirin na tsawon shekaru 11 a jihar Kaduna.

Gwamna Uba Sani ya dawo da shirin daukar nauyin sauke faralin Kiristoci
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce shugabar ma’aikata ta gwamnatin jihar Kaduna, Jimami C. Bako, ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi a wurin taron bitar shekarar 2025 ga maniyyata Kiristoci 50 da gwamnati ta dauki nauyi.

Kara karanta wannan

Kano: Manyan mutane da suka ziyarci kasuwar Singer bayan mummunar gobara

Taron bitar ya nuna karon farko da jihar ta ɗauki nauyin sauke farali na Kiristoci cikin fiye da shekara 11 da dakatar da shi da gwamnatocin baya suka yi.

Gwamna Uba Sani ya samu yabo

Shugabar ma'aikatan ta jihar Kaduna ta yaba wa Gwamna Uba Sani bisa dawo da shirin na daukar nauyin sauke faralin Kiristoci.

Jimami C. Bako ta bayyana cewa gwamnatin ta amince da cewa bunƙasar ayyukan ibada da kyawawan ɗabi’u muhimman abubuwa ne da ke tafiya tare da samar da ababen more rayuwa da ci gaban tattalin arziki.

Ta kara da cewa farfaɗo da shirin sauke faralin ya nuna irin salon shugabanci ne da ke ɗaukar addini a matsayin ginshikin zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

Kwamishinan yaɗa labarai, Ahmed Maiyaki, ya bayyana cewa wannan matakin ya yi daidai da ƙudurin gwamnatin na samar da adalci, daidaito, da kuma tafiya tare da kowa da kowa ba tare da la’akari da addini ba.

An ba wadanda suka amfana shawara

Kwamishinan ya buƙaci maniyyatan da su yi amfani da wannan dama su yi addu’ar neman zaman lafiya, haɗin kai, da dorewar arziki a jiha da ma kasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Aminu Vs Sanusi II: Gwamna Abba ya sake tabo batun rikicin sarautar Kano a gaban Sanata Barau

Ga waɗanda suka amfana, dawo da shirin sauke faralin ya zama alama ta sabon fata, karfafa amincewa ga gwamnatin jiha, da kuma karfafa zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban a Kaduna.

Gwamnatin Kaduna ta dawo da daukar nauyin sauke faralin Kiristoci
Sanata Uba Sani, gwamnan jihar Kaduna Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta ce a watan Nuwamba na shekarar 2014, maniyyata Kiristoci 567 daga Kaduna ne aka kwashe daga filin jirgin saman jihar zuwa kasar Isra’ila.

Yayin da yake jawabi a filin jirgin saman lokacin da suke tashi, Ramalan Yero, wanda shi ne gwamnan jihar a lokacin, ya buƙaci maniyyatan da su kasance jakadu nagari na Najeriya yayin da suke a Isra'ila.

Tinubu ya ba Uba Sani mukami

A wani labarin kuma, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna a wani muhimmin mukami.

Mai girma Bola Tinubu ya ya nada Uba Sani jakadan "Renewed Hope" kuma Mataimakin darakta-janar na hulɗa da jama'a da wayar da kai na jam'iyyar APC.

Manufar Tinubu ta yin nadin ita ce tabbatar da cewa daukacin ƴan ƙasa sun san manufofin jam'iyyar APC tare da goya mata baya a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng