Ramadan: Gwamnatin Kano Ta Kara Azama wajen Toshe 'Kofofin Badala'
- Hukumar tace fina-finai ta Kano ta umarci rufe duk wuraren nishaɗi daga 18 ga Fabrairu, 2026 a baki daya fadin jihar saboda azumin Ramadan
- Hukumar ta bayyana cewa wannan umarni zai shafi gidajen gala da masu DJ da ke cinikayyarsu a sassa daban-daban na Kano
- A sanarwar da ta fitar, hukumar tace fina-finai ta ce wannan zai taimaka wajen tabbatar da cewa jama'a sun yi azumi a cikin lumana
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Hukumar tace fina-finai ta Kano ta bayar da umarnin dakatar da dukkannin harkokin nishaɗi a faɗin jihar har zuwa ƙarshen watan azumin Ramadan.
Hukumar ta bayyana cewa wannan mataki ya haɗa da rufe dakunan taro da ake kira gidan gala da kuma masu kaɗe-kade wato DJ. .

Kara karanta wannan
Ana jiran sanarwar Sarkin Musulmi, gwamnatin Kano ta ba da shawarwari 4 kan azumin Ramadan

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata.
Gwamnatin Kano ta rufe gidajen nishadi
Jaridar PoliticsNigeria ta ruwaito a cewarsa, umarnin zai fara aiki ne daga ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026, da 10:00 na dare.
Hukumar ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin bai wa al’ummar Musulmi damar gudanar da azumin watan Ramadan da sauran ibadunsu cikin yanayi na nutsuwa.
Sanarwar ta ce dukkannin wuraren nishaɗin za su ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa ƙarshen watan azumi.

Source: Original
Haka kuma, hukumar ta ce za a sanar da ranar da za a buɗe su, musamman yayin bukukuwan Sallah, a lokacin da ya dace.
A cewar hukumar, wannan mataki na daga cikin nauyin da doka ta ɗora mata na kula da yadda ake tafiyar da harkokin nishaɗi a jihar Kano.
Hukumar tace fina-finai ta yi gargadi a Kano
Hukumar tace fina-finai ta kuma yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su ba da cikakken haɗin kai tare da bin wannan umarni kamar yadda doka ta tanada.
Ta jaddada cewa za a ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda ya saɓa wa wannan umarni bayan ya fara aiki.
An kuma roƙi al’umma da su yi amfani da wannan lokaci wajen ƙara himma a ibada, tare da wanzar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin jama’a.
Hukumar ta yi addu’ar Allah Ya sa a gudanar da watan Ramadan cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali, tare da bai wa kowa damar samun falalar wannan wata mai albarka cikin rahama da wadata.
Abba zai yi rabon kayan azumi a Kano
A baya, mun wallafa cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon kayan azumi domin saukaka wa mutane a lokacin watan Ramadan a fadin Kano.
Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin raba buhunan shinkafa ga dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar Kano Gwamnan ya kuma kafa kwamitoci da su sanya ido kan rabon.
Gwamnan na jihar Kano ya bayyana aikin a matsayin tsohuwar al’ada ta kowace shekara da nufin taimaka wa gajiyayyu a lokacin watan alfarma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

