El Rufai Ya Shafe Kwanaki 2 a Hannun EFCC, Lauyansa Ya Fadi Shirin da Ke Ƙasa
- Tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya sake kwana a hannun hukumar EFCC yayin da ake gudanar da bincike kan zargin bacewar N432bn
- Lauyan Nasir El-Rufai ya bayyana cewa wanda yake karewa mutum ne mai daraja wanda ya dawo gida Najeriya don amsa gayyatar EFCC
- An ce EFCC na shirin neman izinin kotu domin tsawaita tsare tsohon gwamnan da nufin kara titsiye shi kan zarge-zargen da ake yi masa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Ya zuwa ranar Laraba, tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shafe dare na biyu a hannun hukumar EFCC, yayin da lauyansa, A.U Mustapha (SAN), ke neman a sake shi.
Akwai alamun cewa hukumar na iya neman izinin kotu domin tsawaita tsare tsohon gwamnan don ba shi damar amsa ƙarin tambayoyi kan zargin almundahanar ₦432bn.

Source: Twitter
EFCC na shirin tsawaita tsare Nasir El Rufai
Tsohon gwamnan ya isa hedikwatar EFCC da ke Abuja ne da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Litinin, inda jami’ai suka fara yi masa tambayoyi har zuwa yau, cewar rahoton Daily Trust.
Wani jami’in hukumar wanda ya buƙaci a sakaye sunansa, ya bayyana cewa EFCC na duba yiwuwar samun izinin kotu bayan cikar sa'o'i 48 da doka ta ba su na tsare mutum.
Jami'in EFCC ya ce:
"Ku manta da jita-jitar da ake yaɗawa a kafofin sada zumunta cewa an sake shi. Har yanzu El-Rufai yana hannunmu kuma zai ƙara kwana a tsare.
"Masu bincike suna buƙatar ƙarin lokaci tare da shi domin ya amsa tambayoyi game da shekaru takwas da ya yi yana mulki a jihar Kaduna."
Binciken hukumar EFCC yana da alaƙa da rahoton kwamitin bincike na Majalisar Dokokin Jihar Kaduna da aka kafa a shekarar 2024 don bincikar kwangiloli da rancen kudade tsakanin 2015 zuwa 2023.
Lauyan El-Rufai zai nemi beli
Lauyan El-Rufai, A.U Mustapha, ya tabbatar da cewa wanda yake karewa yana nan a hannun hukumar, inda ya jaddada cewa tsohon gwamnan yana ba da cikakken haɗin kai.
A zantawarsa da jaridar Punch, A.U Mustapha ya ce:
"A matsayinsa na mai kishin ƙasa, an gayyace shi kuma ya amsa gayyatar. Yana ba da haɗin kai iyakar iyawarsa, kuma muna fatan EFCC za ta ba shi beli.
"Mutum ne mai gaskiya wanda kowa ya sani. Ya dawo Najeriya da kansa kuma ya rubuta wasiƙa cewa zai amsa gayyatar EFCC, kuma ya cika alkawarinsa."
Mustapha ya ƙi yin bayani kan takamaiman zargin da ake yi wa tsohon gwamnan, inda ya ce hakan sirri ne na bincike kuma EFCC ce kaɗai za ta iya yin bayani a kai.

Source: Facebook
Binciken da ake yi kan El-Rufai
Ana zargin El-Rufai da karkatar da kudaden jihar ta hanyar kwangiloli da kuma bashin da aka karɓa lokacin da yake kan mulki, kamar yadda majalisar jihar ta yi zargi.
Majalisar jihar Kaduna ta yi ikirarin cewa an yi sama da fadi da maƙudan kuɗaɗe waɗanda aka ware don ayyukan raya ƙasa, zargin da El-Rufai ya sha musantawa tun da fari.
A halin yanzu, magoya bayansa da lauyoyinsa na dako domin ganin ko hukumar za ta amince da belinsa ko kuma za ta garzaya kotu domin neman ƙarin lokacin tsare shi.
Zabi 2 da suka rage wa El-Rufai
A wani labari, mun ruwaito cewa, lauya kuma masani kan harkokin tsaro, Bulama Bukarti, ya ce tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya sa kansa a matsala.
Barista Bulama Bukarti ya ce tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya furta kalaman da ke nuna ya saurari kiran wayar Malam Nuhu Ribadu ba bisa ka'ida ba.
Lauyan ya ce ko da an ce kuskure ne, zabi biyu ya rage wa El-Rufa'i a kan wannan matsala a kotu, kuma dukkaninsu ba masu dadi ba ne ga babban 'dan siyasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


