Masu Daukar Nauyin Ta’addanci Sun Shiga Uku, UN Ta Magantu kan Kashe Musulmi
- Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakkausar suka kan harin ta’addanci a Kwara da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 160
- Majalisar ta bukaci a cafke masu hannu a harin tare da hukunta masu daukar nauyinsu bisa doka, tare da hadin gwiwa da gwamnatin Najeriya
- Harin ya shafi al’ummomin Nuku da Woro, inda aka sace mata da yara tare da lalata dukiyoyi mutane da ya jawo mummuan nasara a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kwamitin Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da harin ta’addanci da aka kai a jihar Kwara.
Kwamitin ya nuna damuwa kan harin wanda ya yi sanadin mutuwar kusan Musulmi 200 da ya tayar da kura a fadin kasar.

Source: Twitter
Majalisar Dinkin Duniya ta magantu kan harin Kwara
Mambobin majalisar sun bayyana harin a matsayin “mugun aiki kuma na rashin tausayi”, inda suka jaddada bukatar hukunta duk wadanda suka shirya, suka dauki nauyi ko suka tallafa wa harin, kamar yadda aka wallafa a shafinta na yanar gizo.
An kai hare-haren ne a garuruwan Nuku da Woro a ranar 3 ga Fabrairun 2026, lamarin da ya haddasa sace mata da yara da dama tare da lalata dukiyoyi.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a birnin New York, Majalisar ta sake jaddada cewa ta’addanci a kowane irin salo babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron duniya.

Source: Original
Hare-haren ta'addanci: Bukatar Majalisar ga gwamnatin Najeriya
Majalisar ta bukaci dukkan kasashe su hada kai da gwamnatin Najeriya domin cafke masu hannu a lamarin tare da tabbatar da an gurfanar da su gaban kuliya.
Ta kuma sake nanata cewa duk wasu ayyukan ta’addanci laifi ne kuma ba shi da wani uzuri, komai dalilin da aka bayar ko wanda ya aikata shi.
Kwamitin ya ce:
“Mambobin Kwamitin Tsaro sun sake jaddada cewa dukkan ayyukan ta’addanci laifi ne kuma ba su da wani hujja, ba tare da la’akari da dalilinsu ba, a ko’ina, a kowane lokaci, kuma daga duk wanda ya aikata su.”

Kara karanta wannan
Rigimar da ta kaure a Majalisar wakilai ta kara tsanani, wasu yan majalisa sun yi fushi
Majalisar ta bayyana alhininta ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tare da jajantawa gwamnati da al’ummar Najeriya baki daya.
Haka kuma ta yi addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata tare da kira da a sako wadanda aka sace cikin koshin lafiya.
Yan bindiga sun saki bidiyon wadanda suka sace
A baya, kun ji cewa wasu yan ta'adda sun saki bidiyon mutane 176 da suka sace a garin Woro dake jihar Kwara kuma suke ci gaba da tsare su har zuwa wannan lokaci.
A cikin bidiyon, an jiyo mutanen da aka sacen, wadanda mafi yawansu mata da kananan yara ne, suna neman daukin gaggawa daga gwamnati domin ceto su daga miyagun.
Al'ummar garin Woro, sun ce 'yan bindigar sun dade suna masu barazana, a karshe suka kai masu hari mafi muni a tarihin garin wanda ya tayar da kura a fadin Najeriya baki daya.
Asali: Legit.ng
