Majalisar Dattawa Ta Ji Koken Musulmai, Ta Gyara Dokar Zabe saboda Azumin Ramadan

Majalisar Dattawa Ta Ji Koken Musulmai, Ta Gyara Dokar Zabe saboda Azumin Ramadan

  • Majalisar dattawa ta saurari koken yan Najeriya kan sanya ranakun babban zaben 2027 a watan azumin Ramadan na badi
  • A zaman da ta yi yau Talata, Majalisar ta gyara sashen da zai ba hukumar INEC damar canza ranakun da ta sanar idan da bukatar hakan
  • Haka zalika yunkurin Sanata Enyinna Abaribe na gyara tanadin dokar tura sakamakon zabe ta intanet bai yi nasara ba bayan kada kuri'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Majalisar dattawan Najeriya ta sake yin gyara a dokar zabe biyo bayan korafe-korafen da musulmai suka yi kan sanya ranakun zaben 2027 a watan azumin Ramadan.

Majalisar Dattawa ta gyara sashe na 28(1) na Kudurin Dokar Zaɓe da aka yi wa gyara ta 2026, wanda zai bai wa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) damar yin gyara a jadawalin zaɓe.

Kara karanta wannan

Rigimar da ta kaure a Majalisar wakilai ta kara tsanani, wasu yan majalisa sun yi fushi

Majalisar dattawa.
Sanataci yayin da suke tsaka da zama a zauren Majalisar dattawa Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an samu koke-koke kan yadda azumin Ramadan zai ci karo da babban zaɓen 2027.

Mutane da dama, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, sun buƙaci INEC ta sake nazari kan lamarin.

A ranar Talata, Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Bamidele Michael Opeyemi, ya gabatar da kuduri mai taken, “Sake Gyara Kudurin Dokar Zaɓe ta 2026”.

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan INEC da Harkokin Zaɓe, Sanata Simon Lalong, ya mara wa kudurin baya, kamar yadda tashar Channels tv ta kawo.

Majalisa ta gyara sashen sanarwar zaɓe

Sashen da aka gyara, wanda ya shafi “Sanarwar Zaɓe”, ya tanadi cewa:

“Hukumar INEC za ta fitar da sanarwar zaɓe a kowace jiha da Babban Birnin Tarayya ƙasa da kwanaki 300 kafin ranar da aka ware domin gudanar da zaɓe.”

A baya, dokar asali ta tanadi kwanaki 360 kafin zaɓe. Sabon gyaran zai bai wa INEC damar matsar da jadawalin zaɓe gaba idan akwai buƙata.

Kara karanta wannan

An fadi ranar da ake hasashe za a dawo da zaben 2027 bayan korafin Musulmai

A ranar Juma’a, INEC ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Tarayya a ranar 20 ga Fabrairu, 2027, yayin da zaɓen gwamnonin jihohi da ’yan majalisun jihohi zai gudana a ranar 6 ga Maris, 2027.

An yi yunkurin dawo da batun sashe na 60 (3)

Bayan Sanata Eyinnaya Abaribe ya nemi a raba gardama kan sashe na 60(3), wanda ya amince da tura sakamakon zaɓe ta intanet da kuma takarda, Akpabio ya jagoranci kada kuri'a don yanke shawarar karshe.

Akpabio.
Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Sanatoci 55 sun goyi bayan matsayin Majalisar Dattawa na makon da ya gabata, yayin da sanatoci 15 suka nemi a rungumi sigar da majalisar ta gabatar a baya, wadda ta tanadi tura sakamakon zaɓe kai tsaye daga kowace rumfa.

Majalisa dattawa ta amince da tura sakamako

A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta sauya matsayarta kan kin amincewa da tanadin tura sakamakon zabe kai tsaye ta hanyar yanar gizo.

Majalisar dattawan ta janye matsayar da ta cimma a baya na kin amincewa da tura sakamakon zabe kai-tsaye daga rumfunan zabe.

Bayan tattare wuri, Majalisa ta amince da tura sakamakon zabe ta na'ura tare da na takarda, ta yi fatali da bukatar turawa sakamakon kai tsaye.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262