Kudirin Kafa Hisbah na Shirin Gamo da Matsala a Niger, CAN Ta Tsoma Baki

Kudirin Kafa Hisbah na Shirin Gamo da Matsala a Niger, CAN Ta Tsoma Baki

  • Ƙungiyar CAN ta jihar Niger ta yi ƙorafi kan kudirin kafa dokar Hisbah, tana cewa zai haifar da wariya ga Kiristoci
  • Shugaban CAN, Bulus Dauwa Yohanna, ya roƙi Gwamna Mohammed Umaru Bago kada ya rattaba hannu kan kudirin
  • CAN ta yi gargaɗin cewa dokar na iya karya kundin tsarin mulkin Najeriya tare da haddasa rabuwar kai a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen jihar Niger, ta yi magana kan shirin kafa hukumar Hisbah da ake yi.

Kungiyar CAN ta nuna damuwa kan kudirin dokar da Majalisar Dokokin Jihar ke shirin amincewa da shi, tana mai cewa hakan na iya janyo wariya da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummar jihar.

CAN ta magantu kan shirin kafa Hisbah a Niger
Taswirar jihar Niger da ake shirin kafa hukumar Hisbah. Hoto: Legit.
Source: Original

CAN ta soki shirin kafa hukumar Hisbah

Hakan na cikin wata sanarwa da aka fitar a Minna, wadda Shugaban CAN na jihar, Rabaran Bulus Dauwa Yohanna, ya sanya wa hannu, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Majalisar shari'ar Najeriya ta shiga wa Kwankwaso fada da Amurka

Kungiyar ta bayyana cewa kudirin dokar Hisbah da ɗan majalisar Chanchaga, Hon. Mohammed Abubakar ya gabatar, kudiri ne mai tayar da ƙura wanda bai kamata bangaren zartarwa ya amince da shi ba.

CAN ta buƙaci Kakakin Majalisar Dokoki da sauran mambobi da su janye kudirin idan ba manufarsu ba ce tayar da hankalin wani ɓangare na jama’a a jihar.

CAN ta roki Gwaman Bago kan shirin kafa Hisbah
Gwamna Mohammed Bago na jihar Niger. Hoto: Mohammed Umaru Bago.
Source: Twitter

Bukatar kungiyar CAN ga Gwamna Bago a Niger

Sanarwar ta yi kira ga Gwamna Mohammed Umaru Bago da ya yi la’akari da abin da ka iya haifar da rabuwar kai a tsakanin al’ummar da yake jagoranta, tana mai cewa lamarin na buƙatar kulawa ta gaggawa.

Shugaban CAN, wanda shi ne jagoran cocin Katolika na Kontagora, ya tambayi dalilin kafa dokar Hisbah a jihar Niger, yana mai cewa ya kamata a fayyace amfanin ta ga tattalin arziki da zamantakewa.

Ya kuma bayyana cewa CAN ba a gayyace ta ko sanar da ita ba dangane da zaman sauraron ra’ayoyin jama’a da aka ce an gudanar, lamarin da ya ƙara nuna wariyar da ake yi wa Kiristoci a muhimman batutuwa.

Yohanna ya jaddada cewa jihar Niger ba ta Musulmi kaɗai ba ce, yana mai kira da a mayar da hankali kan haɗin kai maimakon abin da zai iya rarraba al’umma.

Kara karanta wannan

Kano: Manyan mutane da suka ziyarci kasuwar Singer bayan mummunar gobara

Ya roƙi gwamnan da kada ya rattaba hannu kan kudirin domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a jihar, cewar Daily Post.

Sanarwar ta ƙara da cewa dokar Hisbah za ta iya tauye haƙƙin waɗanda ba Musulmi ba, tare da sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya wanda shi ne doka mafi girma a ƙasa.

CAN ta gargaɗi cewa aiwatar da dokar zai iya zama wata hanya ta muzgunawa Kiristoci da tauye ’yancin addini, tana mai kira ga ’yan Najeriya masu kishin ƙasa su tashi tsaye domin ganin kudirin bai zama doka ba.

Auren wasa: Hisbah ta kama matasa a Kano

Kun ji cewa Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama matasa biyar bisa zargin yin aure ba tare da amincewar iyayensu ba.

Rahoto ya ce cikin wadanda aka kama akwai amarya, ango, da wasu uku da suka shiga wajen shaidar aure ba tare da tsari ba.

Hisbah ta byyana cewa an yi auren ne bisa biyan sadaki na ₦10,000 wanda bai kai ka’idar yadda Musulunci ya tanada ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.