Magudi: Limamin Coci Ya Fadi Amfanin Yin Zabe Ana Azumi a Watan Ramadan
- Wani malamin addini, Sam Olu-Alo, ya goyi bayan jadawalin zaɓen 2027, yana mai fadan fa'idar yin zaben a watan azumi
- Malamin ya ce gudanar da zaɓe a lokacin azumin Musulmi zai ƙara tsoron Allah da gaskiya ga masu zaɓe da ’yan siyasa
- Ya roƙi ’yan Najeriya su guji nuna wariyar addini, su mai da hankali kan zaman lafiya da haɗin kai yayin zaɓukan 2027
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wani malamin addini a Najeriya, Fasto Sam Olu Alo, ya yi magana bayan Musulmi na neman sauya ranar zabe saboda Ramadan.
Fasto Alo ya nuna goyon bayansa ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) kan ranar da ta sanya domin gudanar da babban zaɓen shekarar 2027.

Source: Facebook
Malamin ya bayyana cewa gudanar da zaɓe a lokacin azumin Musulmi zai kasance alheri ga ƙasa baki ɗaya, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Jerin sharudda 15 da Sarkin Musulmi ya gindaya wa malaman da za su yi tafsiri a Ramadan
Ya jaddada cewa irin wannan lokaci mai tsarki zai taimaka wajen rage magudin zaɓe tare da ƙarfafa gaskiya a tsakanin masu kaɗa ƙuri’a da ’yan siyasa.
Ranar da hukumar zabe ta sanya
Legit Hausa ta ruwaito cewa INEC ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, ’yan Majalisar Tarayya a ranar 20 ga Fabrairu, 2027, yayin da na gwamnoni da ’yan Majalisun Jihohi za su gudana a ranar 6 ga Maris, 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana jadawalin zaɓen a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja.

Source: Facebook
Fasto ya soki masu korafi kan ranar zabe
Bayan kammala azumi da addu’o’in kwanaki 41 na cocinsa, Olu Alo ya yi watsi da korafe-korafen da wasu ke yi kan gudanar da zaɓe a lokacin azumi.
Ya ce:
“A lokacin azumi muna ƙarfafa gaskiya, kuma hakan ba zai ba mu damar murɗe abubuwa ba. Ina ganin ya dace a gudanar da zaɓe a lokacin azumi domin hakan zai taimaka mana mu zaɓi shugabanninmu cikin addu’a.”
Ya ƙara da cewa bai kamata a tada jijiyoyin wuya ba kan ranar da aka sanya domin babban zaɓen ba, yana mai cewa an taɓa gudanar da zaɓe a lokacin azumin Kiristoci ba tare da wata hayaniya ba.
A cewarsa, bai kamata a ɗaga murya ba idan jadawalin ya faɗa a lokacin azumin Musulmi, domin hakan ma zai taimaka wajen gudanar da zaɓe cikin tsoron Allah da gaskiya, ba tare da nuna wariyar addini ba, cewar The Guardian.
Yadda INEC ta sauya ranar zabe saboda Kiristoci
Mun ba lu labarin cewa an tuna yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta sauya lokacin zabe bayan Kiristoci sun yi korafi.
A shekarar 2003, INEC ta sauya ranar zaben gwamna da majalisar jiha bayan korafin Fastoci na Katolika kan karo da bikin Easter.
Kungiyar CBCN ta ce sanya zabe a ranar Asabar Mai Tsarki ya nuna rashin la’akari da mabiya Kirista masu bin addinin da ibada sau da kafa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
