Gobarar Singer: An Gano Biliyoyin Naira da Tinubu, Gwamnonin APC Suka ba Kano

Gobarar Singer: An Gano Biliyoyin Naira da Tinubu, Gwamnonin APC Suka ba Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin APC kan tallafin N8bn da suka ba 'yan kasuwar Singer
  • Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya sanar da tallafin yayin ziyarar jaje da ya kai Kano da kasuwar da ta kone kurmus
  • Wani Nazifi Adam Isa da Legit Hausa ta zanta da shi, ya fadi miliyoyin da suka rasa bayan wutar ta cinye shagonsa da na mahaifinsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jinjina wa Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin jam'iyyar APC bisa damuwar da suka nuna kan iftila'in gobara da aka samu a jihar.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Gwamna Abba ya bayyana ainihin dalilinsa na komawa APC a gaban Shettima

A bayanin da ya yi a ranar Litinin, Abba ya yi godiya ga Tinubu da gwamnonin APC bisa amincewa da bada tallafin ₦8bn ga waɗanda gobarar kasuwar Singer ta shafa.

Gwamnatin tarayya da gwamnonin APC sun ba Kano tallafin N8bn.
Gwamna Abba Yusuf na yi wa Kashim Shettima bayani a kasuwar Singer da ta kone a Kano. Hoto: @officialSKSM
Source: Twitter

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Tofa ya fitar a shafinsa na Facebook, ya bayyana wannan mataki a matsayin gagarumin tallafi ga ƴan kasuwar.

Tinubu, gwamnonin APC sun kai tallafi Kano

Abba Kabir Yusuf ya ce:

“Wannan tallafi ya ƙunshi ₦5bn daga Gwamnatun Tarayya da kuma ₦3bn daga gwamnonin jam'iyyar APC na faɗin ƙasar nan.”

Yayin da ya ce tallafin ya zo a daidai lokacin da ake bukatarsa, gwamnan ya jaddada cewa kuɗaɗen za su taimaka matuƙa wajen rage raɗadin mummunan asarar da ƴan kasuwar suka yi.”

Kara karanta wannan

Abin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fada da ya koma APC

Ya ƙara da cewa:

"Wannan tallafi ya nuna jajircewar shugaban kasa ga ƴan Najeriya musamman a lokutan da suke neman daukin gaggawa, sannan ina yaba wa gwamnonin APC kan tausayin al'ummata da suka nuna."

Abba Yusuf ya ba da tabbacin cewa za a yi amfani da kuɗaɗen wajen sake gina shagunan da abin ya shafa da kuma ba da agaji kai tsaye ga ainihin waɗanda gobarar ta rutsa da su.

Shettima ya ziyarci kasuwar Singer

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya sanar da wannan gudunmawa yayin ziyarar jaje da ya kai kasuwar Singer, inda ya isar da saƙon goyon bayan gwamnatin tarayya ga waɗanda gobarar ta shafa.

Kara karanta wannan

Manyan jam'iyyar APC da aka gani wajen tarbar gwamna Abba daga NNPP a Kano

Gobarar, wadda ta tashi a ƙarshen mako, ta lalata kayayyaki da kadarori na biliyoyin nairori, wanda hakan ya jefa daruruwan ƴan kasuwa cikin mawuyacin hali.

Shugabannin kasuwar sun kiyasta cewa sama da shaguna 1,000 ne abin ya shafa, inda wasu ƴan kasuwar suka bayar da rahoton mummunar asarar da suka yi.

Gwamna Abba Yusuf ya ce za a yi amfani da kudin da aka samu wajen sake gina shaguna da tallafawa 'yan kasuwa.
Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano zaune a wajen wani taro. Hoto: @Kyusufabba
Source: Twitter

"Mun rasa sama da N30m" - Dan kasuwa

Wani dan kasuwar Singer, Nazifi Adam Isa da wakilin Legit Hausa ta zanta da shi, ya ce sun tafka asara mai yawa, inda shagonsa da na mahaifinsa suka kone kurmus.

Nazifi Isa ya ce:

"Akwai shagona, akwai na mahaifinmu wanda muke ciki, sun kone. Akalla baburan da suka kone a iya jiya da daddare sun kai 200, kekuna ma za su kai 200.
"Dole shi Musulmi zai dauki kaddara a duk yadda tazo masa, amma gaskiya mun ji ba dadi sosai, saboda yanayin yadda 'yan uwa suka shiga alhini marar misaltuwa.
"Mun rasa sama da Naira miliyan 30 a wannan gobara."

Kwankwaso ya jajanta wa yan kasuwar Singer

A wani labari, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya nuna alhini kan obarar da ta tashi a kasuwar Singer da ke Kano a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Kano: Manyan mutane da suka ziyarci kasuwar Singer bayan mummunar gobara

Tsohon gwamnan Kano ya aike da sakon jaje ga ‘yan kasuwar da suka yi asara, yana kira da a kawo daukin gaggawa.

Kwankwaso ya roki hukumomi, jami’an tsaro da masu hannu da shuni su hada kai wajen tallafa wa wadanda abin ya shafa domin saukaka masu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com