Wanda Mahaifinsa Ya Daure Tsirara Ya Zama 'Kwarangwal' bayan Shekara 17

Wanda Mahaifinsa Ya Daure Tsirara Ya Zama 'Kwarangwal' bayan Shekara 17

  • Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta kama wani mahaifi da ta ce ya daure dan shi tsawon shekara 17 saboda zargin cewa ya haukace
  • A lokacin da kakakin 'yan sanda ya shiga dakin da aka daure shi, an samu mutumin tsirara daure da kaca a wani daki ya tara dubun gashi
  • Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ya bayyana cewa sun kai samame gidan ne bayan samun bayanan sirri game da daure mutumin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar ’yan sandan jihar Bauchi ta gano wani mai suna Muhammad Lawan, wanda aka fi sani da Babangida, da mahaifinsa, Mohammed Lawan, ya ɗaure da sarka a jikin itace tsawon shekara 17.

’Yan sandan sun kai samame a gidan da suke a ƙauyen Shadawanka da ke karamar hukumar Bauchi bayan samun rahoton sirri daga wani mazaunin yankin.

Kara karanta wannan

An yi zanga zangar korar 'yan Arewa a Rivers, an fasa shaguna da lalata dukiya

Wanda aka daure wani mutum a Bauchi
Dakin da aka daure wani mutum a jihar Bauchi. Hoto: Nigeria Police Force Bauchi State Command
Source: Facebook

Mahaifi ya daure dansa da sarka

Kakakin rundunar, SP Habib Nafiu, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Facebook, ya ce tawagar rundunar ta ceto mutumin mai matsakaicin shekaru wanda ake zargin mahaifinsa ne ya tsare shi tare da ɗaure masa ƙafafu da sarka.

SP Habibu Nafiu ya ce:

“A ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026, da misalin ƙarfe 4:20 na yamma, mun samu bayani daga wani mutum cewa wani Muhammad Lawan da aka fi sani da Babangida, mahaifinsa Mohammed Lawan ya tsare shi a gidansa tsawon shekara 17 ba tare da kulawa ba.
“Tawagar jami’an bincike ƙarƙashin jagorancin DPO, tare da haɗin gwiwar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar (PPRO), sun ziyarci ƙauyen inda suka samu nasarar ceto wanda aka tsare, wanda ya yi matuƙar ramewa,”

'Yan sandan Bauchi sun kama mahaifin

Rahotanni sun nuna cewa kakakin 'yan sanda, SP Nafiu ya ce an kama mahaifin kuma a halin yanzu yana tsare a hannun ’yan sanda.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga gidan limamin masallacin Izala da dare, sun sace iyalansa

Ya ƙara da cewa an kai wanda aka ceto asibiti domin samun cikakkiyar kulawar lafiya da kuma farfaɗowa, bisa umarnin kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu.

Kwamishinan ya kuma umarci DPO da ya gudanar da bincike kan yadda wannan mummunan aiki ya faru, sannan daga bisani a miƙa shari’ar zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na jiha domin cikakken bincike.

Matashin da aka daure a Bauchi
Gashin kan wanda aka daure a Bauchi. Hoto: Nigeria Police Force Bauchi State Command
Source: Facebook

An samu mutumin tsirara ya rame

A wani bidiyo da kakakin 'yan sandan ya wallafa a Facebook ya bayyana cewa sun samu mutumin a daure tsirara da suka shiga dakin da aka tsare shi.

Mutumin da aka nuna bidiyonsa da dubun gashi ya rame kaman kwarangwal bayan shafe shekaru a cikin daki ba tare da yin ibada ba.

Bayan shiga dakin, kakakin 'yan sanda ya ce:

"Yana tsirara ne ma... Za ku gan shi kamar kwarangwal, amma ba za mu so nuna yanayin shi ba."

'Yan rakiyar amarya sun rasu

A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan rakiyar amarya su 14 sun rasu a wani hadarin jirgin ruwa da ya rutsa da su a karamar hukumar Yauri a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 200 sun shiga garuruwa 3 da Asubah, sun kashe mutane sama da 30

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya bayyana cewa abin da ya faru ya tayar da hankali sosai tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamatan.

Shugaban karamar hukumar Yauri ya bayyana cewa sama da mutum 100 ne a cikin jirgin ruwan da ya kashe mata 13 da yaro guda daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng