An sake gano wani mutum da mahaifinsa ya daure shi a gida na shekaru 30 a Kano (Hotuna)

An sake gano wani mutum da mahaifinsa ya daure shi a gida na shekaru 30 a Kano (Hotuna)

Yan sandan jihar Kano sun ceto wani bawan Allah mai shekaru 55, Murtala Muhammad da mahaifinsa ya rufe shi a daki bayan daure masa kafa na tsawon shekaru 30.

Jamian yan sanda da yan kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Network ne suka ce Muhammad, mazaunin Kofar Fada a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano a ranar Alhamis.

An ce an daure shi ne saboda yana fama da tabin hankali kamar yadda Sahara Reotrers ta ruwaito.

Kano: An sake gano wani mutum da yan uwansa suka daure shi a gida na shekaru 30
Kano: An sake gano wani mutum da yan uwansa suka daure shi a gida na shekaru 30. Hoto daga TVC
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kwanel Assimi Goita ya naɗa kansa shugaban ƙasa na mulkin soja a Mali

Muhammad ya ce ya yi farin ciki da aka cece shi daga halin da mahaifinsa ya jefa shi ciki.

Kwamared AA Haruna Ayagi, Shugaban Human Rights Network ya ce tun lokacin Muhammad yana da shekaru 25 a duniya aka rufe shi a gida aka daure kafarsa a jikin reshen itace.

Kano: An sake gano wani mutum da yan uwansa suka daure shi a gida na shekaru 30
Kano: An sake gano wani mutum da yan uwansa suka daure shi a gida na shekaru 30. Hoto daga TVC
Asali: Twitter

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, Yan sanda a jihar Kano har ila yau sun ceto wani matashi mai shekaru 32, Ahmad Aliyu, wanda mahaifinsa da kishiyar mahaifiyarsa suka kulle tsawon shekaru bakwai a jihar Kano.

Yan sandan sun kai wannan farmaki ne daren Litinin a Farawa Babban Layi, Mariri Quarters a karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Mutumin, wanda hoto da bidiyo suka nuna yana cikin mawuyacin hali ya kwashe kwanaki babu abinci, babu ruwan sha sai dai shan fitsarinsa, HumAngle ta ruwaito.

Wata majiya ta bayyanawa HumAngle cewa mahaifinsa da kishiyar babarsa sun daureshi ne zargin cewa ya fara shaye-shaye da ta'amuni da kwayoyi.

Wata mata mai suna Rahama dake zama a Farawa Babban Layi, Mariri Quarters, ta kaiwa yan sanda rahoto a Farawa kuma kungiyar rajin kare hakkin dan Adam suka garzayo cetonsa.

Yayinda yan sanda da yan kungiyar kare hakkin bil adaman suka isa gidan, kishiyar babar ta ce Ahmad ba ya gida, hakan ya sa suka fasa ciki karfi da yaji suka lalubo shi.

Tuni yan sanda sun damke mahaifin da kishiyar babarsa kuma aka tafi da Ahmad.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel