Babu abinci sai fitsarinsa: An ceto matashin da mahaifinsa da kishiryar mahaifiyarsa suka daure tsawon shekaru 7

Babu abinci sai fitsarinsa: An ceto matashin da mahaifinsa da kishiryar mahaifiyarsa suka daure tsawon shekaru 7

Jami'an yan sanda a jihar Kano sun ceto wani matashi mai shekaru 32, Ahmad Aliyu, wanda mahaifinsa da kishiyar mahaifiyarsa suka kulle tsawon shekaru bakwai a jihar Kano.

Yan sandan sun kai wannan farmaki ne daren Litinin a Farawa Babban Layi, Mariri Quarters a karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Mutumin, wanda hoto da bidiyo suka nuna yana cikin mawuyacin hali ya kwashe kwanaki babu abinci, babu ruwan sha sai dai shan fitsarinsa, HumAngle ta ruwaito.

Wata majiya ta bayyanawa HumAngle cewa mahaifinsa da kishiyar babarsa sun daureshi ne zargin cewa ya fara shaye-shaye da ta'amuni da kwayoyi.

Wata mata mai suna Rahama dake zama a Farawa Babban Layi, Mariri Quarters, ta kaiwa yan sanda rahoto a Farawa kuma kungiyar rajin kare hakkin dan Adam suka garzayo cetonsa.

Yayinda yan sanda da yan kungiyar kare hakkin bil adaman suka isa gidan, kishiyar babar ta ce Ahmad ba ya gida, hakan ya sa suka fasa ciki karfi da yaji suka lalubo shi.

Tuni yan sanda sun damke mahaifin da kishiyar babarsa kuma aka tafi da Ahmad.

KARANTA WANNAN: A fadar shugaban kasa za'ayi daurin auren diyar Buhari da hadimin Fashola

Yan sanda sun ceto matashin da mahaifinsa da kishiryar mahaifiyrasa suka daura tsawon shekaru 7
Ahmad
Asali: Twitter

A wani labarin irin wannan, wata mata ta daure yaro maraya, mai suna Jibril Aliyu, na tsawo shekaru biyu a garken tumaki ba tare da abinci isasshe ba a jihar Kebbi.

Matar uban yaron ta dinga yi mishi tamkar ba dan Adam ba bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani a sa'o'in farko na ranar Litinin, wanda ke nuna yaron a rame har baya iya tashi tsaye saboda yunwa.

Tuni an damke wacce ake zargin yayin da aka kwantar da yaron a asibitin tunawa da Yahaya da ke Birnin Kebbi.

Aliyu Umaru, wanda ya kafe yaro mai shekaru 12 a turken tumaki a jihar Kebbi, ya gurfana a gaban kotu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Nafiu Abubakar, ya bayyana hakan a wata takarda.

Kamar yadda yace: "Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi na sanar da jama'a cewa a ranar 09/08/2020 ne bayani ya riskemu cewa wani Jibrin Aliyu mai shekaru 12 da ke yankin Badariya a Birnin Kebbi an daure shi a garken tumaki da kaji na tsawon shekaru biyu bayan rasuwar mahaifiyarsa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel