Wata Sabuwa: Rigima Ta Kaure a Majalisar Wakilai, An Fara Tayar da Jijiyoyin Wuya a Abuja

Wata Sabuwa: Rigima Ta Kaure a Majalisar Wakilai, An Fara Tayar da Jijiyoyin Wuya a Abuja

  • Mambobin Majalisar wakilai sun barke da hayaniya a zaman gaggawa da aka shirya kan gyaran dokar zaben Najeriya
  • Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya fara ne bayan gabatar da kudirin neman jingine matsayar da Majalisa ta dauka a baya domin sake nazari
  • Kakakin Majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya ayyana shiga zaman sirri domin sulhuntawa da kwantar da hankulan mambobin Majalisa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - An barke da hayaniya a Majalisar Wakilai ta Ƙasa a yau Talata, 17 ga watan Fabrairu, 2025 yayin zaman gaggawa da aka shirya kan gyaran dokokin zaben Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa mambobin majalisar sun barke da hayaniya ne yayin da aka gabatar da kudirin janye matsayar da Majalisar ta dauka a baya kan dokar zabe.

Majalisar Wakilai.
Yan Majalisar wakilai yayin da suke tsakiyar zama a zauren Majalisar tarayya da ke Abuja Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa majalisar wakilai ta kira zaman gaggawa ne domin tattauna batutuwan da suka shafi zaɓe kaɗai gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Majalisar shari'ar Najeriya ta shiga wa Kwankwaso fada da Amurka

Kakakin Majalisa ya yabawa abokan aikinsa

Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, wanda ya jagoranci zaman, ya yaba wa ’yan majalisar da suka taso daga garuruwansu domin halartar abin da ya kira muhimmin aiki na ƙasa.

Ya bayyana cewa zaman na da manufa guda, janye matsayar baya da sake gabatar da Kudurin Gyaran Dokar Zaɓe ta 2025 domin a sake duba shi.

“Abubuwan da ke gabanmu za su tsara yadda zaɓen 2027 zai gudana, tare da bayyana abin da ya kamata a yi,” in ji Abbas.

Shugaban Kwamitin Dokoki da Harkokin Kasuwanci na Majalisa, Hon. Francis Waive, ne ya gabatar da kudurin janye matsayar baya, yana mai jingina da Dokar Tsarin Aikin Majalisa.

Shugaban Kwamitin Harkokin Zaɓe na Majalisa, Hon. Adebayo Balogun, ya mara wa kudurin baya.

Yadda rikici ya barke a Majalisar wakilai

Sai dai rikici ya ɓarke ne lokacin da Kakakin Majalisa, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya nemi a kada kuri’ar murya kan batun soke kudurin gyaran da suka yi a baya.

Kara karanta wannan

Kano: Manyan mutane da suka ziyarci kasuwar Singer bayan mummunar gobara

Yayin da ’yan majalisa da dama suka daga murya da cewa, “A’a!”, Kakakin ya ayyana cewa “Eh!” ne suka rinjaya, tare da buga gudumar Majalisa.

Hakan ya janyo rikici da hayaniya mai zafi a zauren majalisar, inda daga bisani, Kakakin ya ayyana shiga zaman sirri domin dawo da natsuwa da kwanciyar hankali.

Shugaban Majalisar wakilai.
Shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas Hoto: @SpeakerAbbas
Source: Facebook

A halin yanzu, ’yan majalisar wakikan na ci gaba da zama a cikin sirri ba tare da yan jarida ba domin tattaunawa da neman masalaha, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Dokar zabe: An kafa kwamitoci 2 a Majalisa

A wani labarin, kun ji cewa alamu sun nuna an samu sabani a wasu sassan dokar zaben da aka yi wa garambawul a Majalisar dattawa da ta Wakilai.

Sakamakon haka ne majalisun tarayyar sun kafa kwamitoci biyu da za su zauna su duba wadannan banbance-banbance domin a iya daidaita su, saboda gyaran ya zama daya.

Manufar wadannan kwamitoci da Majalisun biyu suka kafa shi ne tabbatar da cewa an samar da gyare-gyaren a dokar zabe da za su ƙara fito da gaskiya, kyakkyawar dabi’a, da kuma ƙarfafa amincewar al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262