Hadiman Gwamna Sun Hakura da Ci daga Jikin Gwamnati, Sun Ajiye Mukamansu
- Gwamnan jihar Ondo, Lukcy Orimisan Aiyedatiwa, ya rasa wasu daga cikin hadimansa a sakamakon yin murabus daga mukamansu
- Hadiman na gwamnan sun yi murabus ne daga mukamansu a cikin wasikun da suka aika na ajiye aiki a karkashin gwamnatin jihar Ondo
- Daya daga cikin hadiman ya nuna godiyarsa kan damar da aka ba shi ta yin aiki a karkashin gwamnatin da Lucky Aiyedatiwa ke jagoranta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ondo - Wasu daga cikin hadiman gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, sun yi murabus daga mukamansu.
Hadiman guda biyu na Gwamna Aiyedatiwa sun yi murabus daga mukamansu na mataimaka na musamman a fannin yaɗa labarai.

Source: Twitter
The Punch ta ce daya daga cikin waɗanda suka yi murabus ɗin, Fasto Taiwo Gbamila, wanda ya yi aiki a matsayin babban mataimaki na musamman ga Gwamna kan kafafen yaɗa labarai na zamani, ya miƙa takardarsa ta ajiye aiki a ranar 16 ga Fabrairu, 2026.
Hadiman gwamnan Ondo sun yi murabus
A cikin wasiƙar da ya aika wa gwamnan, Taiwo Gbamila ya nuna godiyarsa kan damar da aka ba shi na yin hidima a gwamnati, sannan ya sanar da matakinsa na sauka daga mukaminsa.
Jaridar The Nation ta tabbatar da cewa ofishin gwamna ya karɓi wasiƙar tasa a jiya Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026.
Shi ma wani hadimin gwamnan, Olugbenga Abire, ya fice daga gwamnatin, inda ya bayyana matakinsa a fili ta hanyar wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Olugbenga Abire ya bayyana cewa ya sanar da Gwamna Aiyedatiwa matakinsa na yin murabus ne da kansa a ranar Lahadi, 15 ga watan Fabrairun 2026.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi masu addu'a
Ya kara da cewa gwamnan ya yi masa addu’a tare da amincewa da shirinsa na neman sabuwar dama a wani gurin.
Olugbenga Abire ya ce gajeriyar tattaunawar ta su ta ɗauki kusan mintuna shida, inda gwamnan ya yi masa fatan alheri a ayyukansa na gaba.
Ya bayyana cewa ya sanar da murabus ɗinsa da wuri ne domin kauce wa jita-jita, inda ya musanta duk wani zargi game da ficewarsa, yana mai jaddada cewa ya yi hakan ne da son ransa.
"A yammacin ranar Lahadi, 15 ga Fabrairu, 2026, na sanar da Gwamnan Ondo matakin ficewa ta daga gwamnatin jihar, bayan ya naɗa ni domin yi wa al’umma hidima a ranar 23 ga Disamba, 2023."
"A matsayinsa na uba, ya yi mini addu’a kuma ya amince da tsare-tsarena. Haka kuma na sanar da abokan aikina waɗanda su ma suka yi mini fatan alheri."
- Olugbenga Abire

Source: Facebook
Waɗannan murabus ɗin suna zuwa ne a daidai lokacin da ake yada rahotannin cewa akwai yiwuwar samun ƙarin murabus ɗin mataimaka da dama a cikin tawagar yaɗa labarai ta Aiyedatiwa, sakamakon rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da al’amura a halin yanzu.
Gwamna ya kori 'yan majalisar zartarwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da rusa majalisar zartaswar jihar.
Gwamna Siminalayi Fubara ya nuna godiyarsa ga tsofaffin mambobin majalisar bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar.
Hakazalika, gwamnan ya umarci dukkan kwamishinoni da masu ba shi shawara na musamman da su mika ragamar aiki nan take
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

