Rashin Tsaro: Shugaba Tinubu Ya Kwantar da Hankalin 'Yan Najeriya kan 'Yan Bindiga

Rashin Tsaro: Shugaba Tinubu Ya Kwantar da Hankalin 'Yan Najeriya kan 'Yan Bindiga

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a sassa daban-daban na kasar nan
  • Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa gwammatinsa a shirye take wajen gamin ta yi nasara kan 'yan bindiga da 'yan ta'adda
  • Shugaban kasar ya kuma yabawa dakarun tsaron Najeriya kan irin kokarin da suke yi wajen yaki da 'yan bindiga da masu tayar da kayar baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Adamawa - Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Najeriya.

Shugaba Tinubu ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na yin nasara a yakin da ake yi da ayyukan 'yan bindiga da 'yan ta'adda da suka addabi sassa daban-daban na kasar nan.

Shugaba Tinubu ya yi magana kan matsalar rashin tsaro
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta kawo rahoton cewa Shugaba Tinubu ya ba da wannan tabbacin ne a garin Yola ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Ana batun takaddamarsa da El Rufai, Shugaba Tinubu ya aika sako ga Nuhu Ribadu

Shugaba Tinubu ya yabawa jami'an tsaro

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne lokacin da yake kaddamar da ayyukan da Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya gudanar.

Ya jinjina wa kokarin dakarun tsaron Najeriya baki daya, inda ya yi alkawarin ci gaba da ba su dukkan goyon bayan da suke bukata wajen gudanar da ayyukansu.

Me Tinubu ya ce kan rashin tsaro?

“Muna godiya ga dakarun tsaron Najeriya saboda sadaukarwar da suke yi wajen ’yantar da Nijeriya daga 'yan bindiga da masu tada kayar baya. Tare za mu yi nasara."

“Za mu ci gaba da karfafa gwiwar gwamnoninmu, muna kira ga ’yan kasa da su ci gaba da ba su hadin kai dari bisa dari wajen bunkasa jihohinsu da kasa baki daya."

“A matsayina na shugabanku, ina tabbatar muku da ci gaba da yin hidima da sadaukarwa. Najeriya tamu ce, mu ne za mu raya ta. Ni mutum ne mai cike da farin ciki a yau."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Duk da suna jam'iyya 1, tsohon sanatan APC ya kwarewa Tinubu baya

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaban kasar ya yaba wa Gwamna Fintiri kan ayyukan raya kasa da gwamnatin jihar Adamawa ta gudanar.

Shugaba Tinubu ya ba da tabbaci kan rashin tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Shugaba Tinubu ya yabawa Nuhu Ribadu

Haka kuma, Shugaba Tinubu ya yabawa Mai Ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, wanda dan asalin jihar Adamawa ne, inda ya nuna gamsuwa da irin rawar da yake takawa wajen samar da tsaro.

Jaridar TheCable ta ce Tinubu ya bayyana Ribadu, wanda tsohon mataimakin sufeton ’yan sanda ne (AIG) kuma tsohon shugaban hukumar EFCC, a matsayin da wanda jihar Adamawa ke alfahari da shi.

Shugaban ya bayyana a fili cewa, sakamakon jajircewar Ribadu, za a kakkabe dukkan makiya Najeriya daga duk inda suke.

Gwamnatin Tinubu ta ba da tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, ta ba da tallafi ga 'yan kasuwar da gobara ta ritsa da su a Kano.

Kara karanta wannan

'Baki ke yanka wuya,' Hadimin Tinubu ya bukaci a binciki El Rufai kan zargin kutsen waya

Gwamnatin tarayya ta sanar da ba da tallafin Naira biliyan 5 ga mutanen da mummunar gobarar da ta tashi a Kasuwar Singer ta ritsa da su.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya sanar da hakan yayin ziyarar jaje da ya je kai wa a kasuwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng