Ana Batun Takaddamarsa da El Rufai, Shugaba Tinubu Ya Aika Sako ga Nuhu Ribadu
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kwararo yabo ga Mai ba shi shawara kan harkokn tsaro, Malam Nuhu Ribadu
- Mai girma Bola Tinubu ya nuna gamsuwarsa kan irin kokarin da Nuhu Ribadu yake yi wajen jagorantar ayyukan samar da tsaro
- Yabon na shugaban kasar dai na zuwa ne yayin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi zarge-zarge hadimin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Adamawa - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Nuhu Ribadu yana yin "aiki mai kyau" wajen jagorantar yaki da 'yan bindga da ayyukan ta’addanci.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2027 a birnin Yola na jihar Adamawa.
Bola Tinubu ya yabawa Nuhu Ribadu
Mai girma Bola Tinubu ya yi jawabin ne lokacin da yake kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar Adamawa ta kammala, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.
Shugaba Tinubu ya ce yana alfahari da Ribadu kan kokarin da yake yi wajen ayyukan samar da tsaro.
Tinubu ya nuna yakinin cewa kasar za ta yi nasara kan ta’addanci da ayyukan 'yan bindiga karkashin jagorancin Nuhu Ribadu.
“Dole ne na fada a fili a nan cewa kana yin aiki mai kyau kwarai, kuma mun ga sakamakon hakan. Tare da kai, za mu kawar da ’yan bindiga da ’yan ta’adda."
"Kai Mai ba da shawara kan tsaro ne na kasa nagari, mai gaskiya, jajirtacce, mai karfin zuciya, kuma mai sadaukar da kai ga aiki. Na yi amanna jihar Adamawa tana alfahari da kai sosai, domin ni ma ina alfahari da kai."
- Shugaba Bola Tinubu

Source: Twitter
Takaddamar El-Rufai da Nuhu Ribadu
Wannan yabo na Tinubu ga Ribadu yana zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar zarge-zargen da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi wa NSA.
El-Rufai ya zargi ofishin Mai ba da shawara kan tsaro da sayo kusan kilo 10 na sinadarin thallium sulphate.
Ofishin NSA ya musanta wannan zargi, inda ya bukaci El-Rufai da ya mika duk wata shaida da yake da ita ga hukumar DSS domin gudanar da cikakken bincike.
A ranar Alhamis din da ta gabata kuma, jami’an tsaro sun yi yunkurin kama El-Rufai a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, lokacin da ya dawo daga birnin Cairo na kasar Egypt.
Daga baya, El-Rufai ya yi zargin cewa hukumar ICPC ce, bisa umarnin Ribadu, ta bukaci jami’an DSS da su kama shi da zaran ya sauka a kasar.
Ribadu ya gargadi 'yan siyasa
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya ja kunnen 'yan siyasa.
Nuhu Ribadu ya gargadi 'yan siyasar da su guji ayyukan tayar da hankali ko sayen kuri'u a lokacin da ake gudanar da zabe.
Tsohon shugaban na EFCC ya yi gargaɗin cewa za a gano duk wani mutum ko ƙungiya da ke da irin wannan shiri, sannan a hukunta su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

