Gwamnatin Tinubu Ta Tallafawa 'Yan Kasuwar da Suka Yi Asara a Gobarar Kano

Gwamnatin Tinubu Ta Tallafawa 'Yan Kasuwar da Suka Yi Asara a Gobarar Kano

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya je jihar Kano domin jajantawa 'yan kasuwar da gobara ta jawo musu asara
  • Kashim Shettima ya sanar da cewa gobarar wadda ta lakume shaguna masu dumbin yawa babbar masifa ce da ta shafi kasa baki daya
  • Hakazalika, mataimakin shugaban kasar ya sanar da tallafin da gwamnatin tarayya ta ba 'yan kasuwar da mummunar gobarar ta ritsa da su

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta ba da tallafi ga 'yan kasuwar da gobara ta ritsa da su a Kano.

Gwamnatin tarayya ta sanar da ba da tallafin Naira biliyan 5 ga mutanen da gobarar da ta tashi kwanan nan a Kasuwar Singer da ke Kano ta shafa.

Gwamnatin tarayya ta ba da tallafi ga 'yan kasuwar Singer
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ne ya bayyana wannan tallafin a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Barau ya bude kofar bada tallafi, ya mika N100m ga 'yan kasuwar Singer

Kashim Shettima ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar jajantawa da ya kai kasuwar, inda aka yi asarar kayayyaki da dukiyoyi na biliyoyin Naira sakamakon gobarar.

Gobara ta yi barna a Kano

Gobarar wadda ta fara ranar Asabar, ta ci gaba da ci har zuwa ranar Lahadi, inda ta kone shaguna da rumfuna sama da 1,000 a ɗaya daga cikin manyan wuraren kasuwancin Nijeriya.

Hukumar kashe gobara ta ce har yanzu tana gudanar da bincike domin gano sanadin gobarar da kuma girman asarar da ƴan kasuwar suka yi.

Shettima ya jajanta kan gobarar Singer

Mataimakin shugaban kasar wanda ya siffanta lamarin a matsayin babbar masifa, ya ce rashi ne ba ga Jihar Kano kaɗai ba, har ma ga daukacin Najeriya, jaridar Daily Post ta kawo labarin.

Ya yi wa waɗanda abin ya shafa addu’a tare da roƙon Allah da ya kiyaye aukuwar irin wannan masifa a nan gaba.

A yayin ziyarar, mataimakin shugaban ƙasar ya samu rakiyar gwamnonin jihohin Jigawa, Kebbi, da Imo.

Kashim Shettima ya kai ziyara jihar Kano
Kashim Shettima da Gwamna Umar Namadi na Jigawa yayin ziyarar da ya kai jihar Kano Hoto: Garba Muhammad
Source: Facebook

Za a yi adalci wajen rabon tallafin

Shugaban kungiyar ƴan kasuwar Singer, Junaid Zakari, ya jinjina wa gwamnatin Tltarayya kan abin da ya kira tallafi mai kyan gaske wanda ya zo a kan gaba.

Kara karanta wannan

Abin da ake zaton ya jawo gobarar da ta laƙume miliyoyin Naira a kasuwar Singer

Ya tabbatar da cewa za a yi amfani da kuɗaɗen cikin adalci domin tallafa wa ƴan kasuwar da abin ya shafa da kuma farfaɗo da harkokin kasuwanci a kasuwar.

Bayan ziyarar kasuwar, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya wuce zuwa filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata, Kano, domin taron karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf, a hukumance zuwa jam’iyyar APC.

Shugaba Tinubu ya tafi jihar Adamawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tafi wata ziyarar aiki zuwa jihar Adamawa da ke yankin Arewa maso Gabas na Najeriya.

Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da ayyuka da dama a Adamawa ƙasa da sa'o'i 48 bayan ya kai irin wannan ziyarar zuwa jihar Kebbi.

Yayin ziyarar ta yini ɗaya, shugaban zai buɗe manyan ayyuka, ya haɗu da manyan jami'an gwamnati, sannan ya gana da sarakunan gargajiya na jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng