Rikici Ya Barke a Majalisa, An Hana Sanata Natasha Shiga Ofishin Shugaban Kwamiti
- An samu takaddama a majalisar dattawa tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ma'aikatan ofishin Sanata Titus Zam
- Rikicin ya fara ne lokacin da Natasha ta je taron kwamitin majalisa kan hukumar raya Arewa ta Tsakiya, amma ta tarar an gama taron
- Sanata Natasha ta garzaya ofishin Zam, wanda shi ne shugaban kwamitin don jin dalilin cire ta daga taron, lamarin da ya jawo rikici
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - 'Yar majalisa mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta sake shiga wata takaddama a majalisar dattawan kasar nan.
A wannan karon, Sanata Natasha ta tayar da rigimar ne a gabanofishin sanata mai wakiltar Benue ta Arewa maso Yamma, Titus Zam, shugaban kwamitin hukumar raya Arewa ta Tsakiya.

Source: Instagram
An yi taro ba tare da Sanata Natasha ba
Majiyoyi a cikin majalisar sun ce lamarin ya biyo bayan taron kare kasafin kuɗi na kwamitin da aka gudanar a safiyar yau Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026, in ji rahoton Punch.
An ce an gudanar da taron, wanda aka tsara farawa da ƙarfe 10:00 na safe tun kafin isowar Akpoti-Uduaghan, kuma aka tashi ba tare da an jira ta.
Bayan isa wurin da kuma gano an tashi zaman, an ce sanatar ta zarce zuwa wajen magatakardar kwamitin domin sanin dalilin cireta, inda ta samu rakiyar mataimakan ta na majalisa.
Amma an sanar da Natasha cewa magatakardar yana ofishin shugaban kwamitin, Sanata Titus Tartenger Zam. Daga nan ne aka ce ta zarce zuwa ofishin shugaban domin neman ƙarin bayani.
Rigima ta barke a ofishin shugaban kwamiti
Shaidun gani da ido sun yi zargin cewa dambarwar ta tashi ne bayan an hana Natasha shiga ofishin, wanda hakan ya kai ga cacar baki da ya shafi ma’aikata da mutanen da ke cikin tawagar sanatar.
Yayin hargitsin, an zargi ɗaya daga cikin mataimakan sanatar da kai hannu kan wani ma’aikaci da ke ofishin shugaban kwamitin, wanda hakan ya sanya jami’an tsaro shiga tsakani.
Daga ƙarshe jami’an tsaron majalisar tarayyar sun shawo kan lamarin, kodayake ba a samu cikakkun bayanai game da abin da ya haddasa takaddamar ba, in ji rahoton Daily Post.
Natasha ta ce ana nuna wariya a majalisa
An rahoto cewa Sanata Natasha ta nuna rashin amincewa da abin da ta bayyana a matsayin ci gaba da nuna wariya a cikin majalisar dattawa, wanda ya kai ga zargin cire ta daga taron kwamitin.
A cikin wata sanarwa da mataimakinta na yaɗan labarai, Mike Idoko, ya fitar daga baya a Abuja, Natasha ta ce takaddamar ta ƙaru ne lokacin da masu tallafawa shugaban kwamitin suka yi arangama da 'yan tawagar kafofin yaɗan labaranta.
“Kimanin masu tallafawa shugaban kwamitin shida, ciki har da sakataren shugaban, suka ƙwace wayar mai ɗaukar hotona kuma suka furta kalamai marasa dadi. Wannan abin a yi tur ne.”
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
An yi rigima da Natasha a majalisa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi cacar baki mai zafi da shugaban kwamitin kula da harkokin ma'adanai na majalisar dattawa.

Kara karanta wannan
Samha Inuwa: Kotu ta yanke wa fitacciyar jarumar Kannywood hukuncin ɗaurin wata 6
Rahoto ya nuna cewa Sanata Natasha ta nuna fushin ta ne lokacin da shugaban kwamitin, Sanata Patrick Ndubueze ya nemi dakatar da ita lokacin da take magana.
Lamarin ya faru ne a zaman kare kasafin kudin ma'aikatar raya karafa ta Najeriya, wanda ya gudana ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng

