Dakarun Sojoji Sun Kashe Kwamandan Boko Haram, an Kwato Miliyoyin Kudade

Dakarun Sojoji Sun Kashe Kwamandan Boko Haram, an Kwato Miliyoyin Kudade

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara a yakin da suke yi da 'yan ta'adda a yankin Arewa maso Gabas na tsawon shekaru
  • Sojojin sun tare wata mota makare da kudaden da ake zargin suna da alaka da ayyukan ta'addanci a jihar Borno
  • Hakazalika, dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka wani kwamandan kungiyar Boko Haram yayin wani artabu da suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), sun samu nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun tare wata mota inda suka gano tsabar kuɗi kimanin Naira miliyan 37 tare da wasu wayoyin salula da ake zargin suna da alaka da ayyukan ta’addanci a jihar Borno.

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram a Borno
Shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Babban jami’in yaɗa labarai na rundunar OPHK, Laftanar Kanal Sani Uba, ya bayyana a cikin wata sanarwa a shafin Facebook a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Bukarti: Abubuwa 3 da Najeriya za ta kiyaye bayan sojojin Amurka sun sauka Borno

Sojoji sun kwato miliyoyin kudi

Wannan samame, wanda aka gudanar ta hanyar binciken ababen hawa na FOB Chabbal, yana ɗaya daga cikin kokarin da ake yi na ruguza hanyoyin samar da kuɗaɗe da kayan aiki ga kungiyoyin ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Laftanar Kanal Sani Uba ya bayyana cewa an tsare motar, wacce ke ɗauke da mutane biyar, ne yayin gudanar da sintiri na yau da kullum a kan hanyoyin da ’yan ta’adda ke bi.

“Wannan kamun wani babban ci gaba ne a ƙoƙarin da ake na toshe hanyoyin samar da kuɗaɗe da ake zargin ana amfani da su wajen tallafa wa ayyukan ’yan ta’adda."

- Laftanar Kanal Sani Uba

An kashe babban kwamandan Boko Haram

A wani aikin na daban kuma, dakarun OPHK sun dakile wasu hare-hare da ’yan ta’adda suka tsara kai wa al’ummomin Pulka da Mandaragirau a karamar hukumar Gwoza.

Dakarun sun yi wa ’yan ta’addan barna sosai, ciki har da kashe wani babban kwamandan Boko Haram mai suna Abou Aisha, wanda ya samu raunin harbin bindiga a wuyansa.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kai wasikar kai hari kauyuka, mutane sun fara gudu

Sojoji sun kashe kwamandan Boko Haram a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kuma ƙwato manyan makamai da kayan aiki daga hannun tsagerun 'yan ta'addan.

Hakazalika ba a rasa ran soja ko ɗaya ba a fafatawar, sai dai wasu mambobin ƙungiyar sa-kai ta CJTF da ke taimaka wa dakarun sun rasa rayukansu.

An kwashe sojojin da suka ji rauni cikin gaggawa ta hanyar amfani da jiragen rundunar OPHK da na sojojin kasa.

Laftanar Kanal Sani Uba ya siffanta waɗannan ayyuka a matsayin wani ɓangare na dabarun dakile hanyoyin samar da kayayyaki ga ’yan ta’adda da kuma hana su damar yin zirga-zirga yadda suke so.

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun hallaka 'yan ta'adda 16 a hanyar Gidan Kaji da ke kan titin Maiduguri zuwa Damboa a jihar Borno.

Hakazalika, dakarun sun kwace kekuna fiye da 20, da dumbin kayayyaki, makamai, da sauran kayan masarufi wadanda ake amfani da su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng