Jerin Sharudda 15 da Sarkin Musulmi Ya Gindaya Wa Malaman da Za Su Yi Tafsiri a Ramadan
Sokoto, Nigeria - Al'ummar musulmi a ciki da wajen Najeriya na ci gaba da shirye shiryen fara azumin watan Ramadan, wata mai cike da rahama, albarka da gafara.
Tuni Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bukaci a fara duban jinjirin watan Ramadan daga ranar Talata, 29 ga watan Sha'ban, 1447AH daidai da 17 ga Fabrairun 2026.

Source: Facebook
Shafin Daular Usmaniyya na Facebook ya wallafa sanarwar mai dauke da sa hannun sakataren Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Farfesa Ishaq Oloyede.
Sarkin Musulmi ya gindaya sharudda 15
Sai dai, ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) karkashin jagorancin Sarkin Musulmi ta fitar da ƙa’idoji da sharuddan da dole ne malami ya cika kafin fara tafsirin Alƙur’ani.
JNI ta ce ta ƙaruwar malaman da ke gudanar da tafsiri tare da yin habaici, zage-zage da kokarin raba kan musulmai abin damuwa ne ƙwarai.
A cewarta, kamata ya yi tafsiri ya zama hanya ta ilmantarwa da haɗa kan al’umma, ba hanyar haddasa sabani ba da rikici tsakanin mabiya addinin Islama ba.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito kan zargin gwamnati na ba majalisar harkokin Musulunci ta Najeriya makudan kudi
Wannan ne ya sa JNI ta sake jaddada buƙatar bin ƙa’idoji masu tsauri ga duk wanda zai gudanar da tafsiri.
Sharuddan da mai tafsiri ya kamata ya cika
JNI ta bayyana cewa dole ne mai tafsiri ya kasance yana da waɗannan ilimomi da ƙwarewa:
1. Ilimin sanin Alƙur’ani mai girma
2. Ilimin harshen Larabci
3. Fahimtar ilimin sarfu (tsarin kalmomi)
4. Fahimtar ƙa’idojin nahawu da luggar Larabci
5. Fahimtar Balaga
6. Iya bayanin abubuwan da ke ƙunshe a cikin balaga
7. Sanin ayoyi masu kama da juna
8. Sanin ƙira’o’i (nau’o’in karatun Alƙur’ani)
9. Sanin ƙa’idojin wasulla
10. Ilimin aƙida
11. Ilimin fiƙihu da hukunce-hukunce
12. Sanin dalilan saukar ayoyi (Asbābun Nuzūl)
13. Sanin ilimin ayoyin da suka soke wasu (Nāsikh da Mansūkh)
14. Ilimin hadisi
15. Basira da fahimtar yanayin al’ummar da yake wa karatu.
Dalilin Sarkin Musulmi na gindaya sharudda
Sakatare-Janar na JNI, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa ba sabon abu ba ne ƙungiyar ta gindaya sharudda, domin tun kimanin shekara 16 da suka gabata aka fara yin hakan.

Kara karanta wannan
Ana zargin an shigo da sinadari mai hadari Najeriya, El Rufai ya aika wasika ga Ribadu
Ya ce sun lura tafsiri na ta ƙaruwa a Najeriya, amma ci gaban ya zo da wasu sauye-sauye da suka sa aka fara barin asalin tafarkin tafsiri.
A wata hira da BBC Hausa, Farfesa Khalid ya ce:
“Kimanin shekara 16 da suka gabata muka lura tafsiri yana ta haɓaka a Najeriya. Amma haɓakar ta zo da wani sabon salo, inda aka fara kauce wa asalin layin tafsiri,” in ji shi.

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa JNI, wadda ita ce uwar ƙungiyoyin Musulunci a Najeriya ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, tare da wasu manyan sarakuna, ta ga dacewar ɗaukar mataki domin daidaita al’amura.
Izala ta tura malamai wuraren tafsiri
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Izala karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau ta tura malamai jihohi da kasashe tafsirin watan Ramadan na 2026.
Kungiyar Izala ta sanar da haka ne bayan kammala bitar malamai masu tafsiri da ta gudanar a jihar Kaduna a wani bangare na shirin azumin wannan shekara ta 1447AH.
Daga cikin wadanda aka sanar da wuraren za su yi tafsiri akwai shugaban Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau da sakatarensa, Sheikh Kabiru Haruna Gombe.
Asali: Legit.ng