Gaskiya Ta Fito kan Zargin Gwamnati na ba Majalisar Harkokin Musulunci Ta Najeriya Makudan Kudi

Gaskiya Ta Fito kan Zargin Gwamnati na ba Majalisar Harkokin Musulunci Ta Najeriya Makudan Kudi

  • Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta musanta rade-radin cewa gwamnati ke daukar nauyinta ta hanyar ba ta kudade
  • Sakataren NSCIA, Farfesa Farfesa Ishaq Oloyede ya ce babu wata gwamnati a ciki da wajen Najeriya da ta taba ba su tallafin kudi
  • Ya kuma yi kira da a daina jinginawa musulunci ayyukan da 'yan ta'adda ke yi, yana mai cewa matsalar tsaron Najeriya ba ta da alaka da addini

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta musanta karbar kudi daga hannun gwamnati domin gudanar da ayyukanta.

Sakataren Janar na NSCIA ta kasa, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewa babu wata gwamnati, a cikin Najeriya ko waje, da ta taɓa bai wa ƙungiyar tallafin kuɗi.

Sarkin Musulmi.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III a fadarsa da ke Sakkwato Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Facebook

NSCIA na samun tallafi daga gwamnati?

Kara karanta wannan

Jerin sharudda 15 da Sarkin Musulmi ya gindaya wa malaman da za su yi tafsiri a Ramadan

Daily Trust ta rahoto cewa Oloyede, ya bayyana hakan ne a Legas yayin laccar shirin azumin Ramadan ta 31 da ƙungiyar tsofaffin ɗalibai Musulmi ta Jami’ar Legas (UMA) ta shirya.

Farfesa Oloyede, wanda shi ne shugaban hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ya ce a shekaru 15 da ya shafe yana sakataren NSCIA, majalisar ba ta taɓa karɓar “ko sisi ɗaya” daga kowace gwamnati ba.

Ya ƙara da cewa tun daga 2013, mutane ƙasa da 20 ne kawai suka taɓa bayar da gudummawar har Naira 500,000 ga majalisar, yana mai jaddada cewa ƙungiyar na aiki ne ba tare da wani tallafin kudi daga waje ba.

Oloyede ya nuna damuwa kan abin da ya kira yaɗa bayanan ƙarya da rabuwar kai tsakanin musulmi game da NSCIA a ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi, Muhammad Saad Abubakar.

Shin matsalar tsaro na da alaka da musulunci?

Da yake jawabi kan taken “Mahangar Musulunci kan Kalubalen Tsaron Ƙasa,” ya yi gargadin cewa bai kamata a riƙa kallon matsalolin tsaro, ta’addanci da ayyukan ’yan bindiga ta fuskar addini ba.

Kara karanta wannan

Ana ruguza allunan tallata Tinubu a Zamfara, ran jam'iyyar APC ya baci

Ya ce masu tayar da kayar baya kan yi amfani da kalaman addini ne kawai domin su halasta ayyukansu, amma hakan ba ya nufin addinin Musulunci ne ya haifar da su ba.

“Ba za a iya jinginawa Musulunci abin da waɗancan mutane ke faɗa ba. Wajibi ne mu gyara wannan fahimta,” in ji shi.
Farfesa Oloyede.
Sakataren Majalisar Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya kuma shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede Hoto: @JAMBHQ
Source: Twitter

Ya jaddada cewa tsaro na daga cikin ginshiƙan Shari’a, yana mai cewa Musulmi na gaskiya shi ne wanda maƙwabtansa, ko wane addini suke bi, ke tsira daga cutarsa, in ji rahoton Guardian.

Ya kuma yi gargadin cewa bai kamata a mayar da matsalar tsaro ta zama ta wani yanki ko addini kaɗai ba, domin dukkan sassan ƙasar na fuskantar ƙalubalen tsaro.

Sarkin Musulmi ya nemi a duba watan Ramadan

A wani labarin, kun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana cewa za a fara duba jinjirin watan Ramadan na shekarar 1447/2026 da yammacin ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026.

A cewar sanarwar Sarkin Musulmi ya rattaba hannu, idan an ga jinjirin watan a ranar Talata, 17 ga Fabrairu, azumin Ramadan zai fara ne a ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026.

Kwamitin duba wata na kasa (NMSC), tare da haɗin gwiwar Hukumar NASRDA sun shirya tsare-tsare domin gudanar da duban watan a hukumance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262