Ana Shirin Fara Azumi, Naira Ta Tumurmusa Dalar Amurka a Kasuwar Canjin Kudi
- Darajar Naira ta kara karfi a ranar Litinin, inda ake yi cinikinta kasa a N1,400 sabanin yadda aka yi hada-hadarta a makonnin jiya
- CBN ya dauki matakan samar da dala a kasuwannin canji, wanda ake ganin ya taimaka wajen daidaita darajar Naira a kasuwar canji
- Masana sun bayyana cewa samuwar dala ga 'yan canji ta taimaka wajen rage matsin lambar da kasuwar gwamnati ke fuskanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Legas - Kudin Najeriya, watau Naira, ya shiga mako na uku na watan Fabrairun 2026 da karfinsa, inda yake ci gaba da rike darajar da ya samu kan dalar Amurka a baya bayan nan.
Yayin da kasuwar musayar kudi ta bude a ranar Litinin, Naira ta ci gaba da daidaita karfinta, sakamakon matakan samar da dala da CBN ya ɗauka domin daƙile buƙatun masu nema.

Source: Getty Images
Wannan nasara ta biyo bayan yadda Naira ta daddage ta ragargaji dala zuwa kasa da 1400 da aka dade ana musayar kudin a cikin makonnin da suka gabata, in ji rahoton Vanguard.
Farashin Naira kan Dala a kasuwar gwamnati
A kasuwar musayar kudi ta Najeriya (NFEM), An fara hada-hadar kudin Naira a farkon makon nan a farashin N1353.54 kan kowace dalar Amurka.
Yayin da lokaci ya fara tafiya, sai aka samu wani dan karamin sauyi, inda aka dawo hada-hadar Naira a farashin N1354.15 kan kowace dala.
Masana tattalin arziki sun danganta wannan nasarar da manufofin Babban Bankin Najeriya (CBN) na yin amfani da tsarin musayar kudi ta EFEMS.
Hanyoyin da suka taimaka Naira ta yi karfi
Haka zalika, shawarar da aka ɗauka na ƙara yawan dala a hannun ƴan canji (BDC) ya taimaka wajen rage matsin lambar da kasuwar gwamnati ke fuskanta.
Wannan matakin ya taimaka wajen tabbatar da cewa dalar tana isa ga masu buƙarta cikin sauƙi ba tare da samun cikas ko tsaiko a fannin ba.

Kara karanta wannan
Samha Inuwa: Kotu ta yanke wa fitacciyar jarumar Kannywood hukuncin ɗaurin wata 6
Wannan tsari na CBN ya taimaka wajen gano ainihin farashin canji na gaskiya, wanda hakan ya rage yawan tsoro da fargaba a tsakanin masu zuba jari.

Source: Getty Images
Farashin Naira a kasuwar bayan fage
A kasuwar bayan fage kuwa, an samu 'yar tazarar farashi na musayar Naira zuwa Dala idan aka kwatanta da farashin kasuwar gwamnati.
A manyan wuraren 'yan canji da ke Legas, Abuja da Kano, ƴan canji sun bayyana cewa ana cinikin dala tsakanin 1420 zuwa 1435 kan kowace Naira.
Rashin tashin farashin a farkon makon nan yana nuna cewa masu harkar canji sun fara gamsuwa da yadda darajar Nairar take a halin yanzu.
Masu canjin kuɗi sun nuna cewa dalar da ake da ita a halin yanzu tana biyan buƙatun mutane a gida da waje da kuma kananan 'yan kasuwa.
Ranar da za a fara azumi a Australia
A wani labari, mun ruwaito cewa majalisar fatawa ta Australia ta sanar da cewa Musulmi a kasar za su tashi da azumin Ramadan a ranar Alhamis.
Majalisar ta shaida cewa ba zai yiwu a ga jinjirin watan Ramadan da ido ko na'urar hangen nesa a ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairu, 2026 ba.
Shugaban majalisar, Ibrahim Mohamad ya bayyana cewa za a fara Sallar Tarawihi a daren Laraba da zarar jinjirin watan Ramadan ya ɓullo.
Asali: Legit.ng
