Bidiyo: Tinubu Ya Kama Hanyar zuwa Adamawa, Shettima Ya Tafi Jihar Kano
- Shugaba Bola Tinubu ya dauki hanyar zuwa jihar Adamawa domin kaddamar da manyan ayyukan raya kasa a ziyarar aiki ta yini daya
- A hannu daya, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya domin jajantawa yan kasuwar Singer dake jihar Kano
- Mataimakin shugaban kasar zai kuma karbi Gwamna Abba Yusuf zuwa jam'iyyar APC bayan ficewarsa daga jam'iyyar NNPP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tafi ziyarar aiki zuwa garin Yola dake jihar Adamawa, yayin da mataimakinsa ya nufi Kano domin jajen gobara.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, zai kuma halarci taron karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa cikin jam'iyyar APC mai mulki a jihar.

Source: Twitter
Tinubu ya kama hanyar zuwa Adamawa
Sunday Dare, mai ba da shawara na musamman ga Tinubu kan watsa labarai ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na X da ya nuna shugaban kasar zai shiga jirgi.
Sanarwar Sunday Dare ta ce:
"Shugaba Bola Tinubu ya kama hanyar Yola a wata ziyarar aiki ta yini daya."
An rahoto cewa Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da ayyuka da dama a Adamawa ƙasa da sa'o'i 48 bayan ya kai irin wannan ziyarar zuwa jihar Kebbi.
Yayin ziyarar ta yini ɗaya, shugaban zai buɗe manyan ayyuka, ya haɗu da manyan jami'an gwamnati, sannan ya gana da sarakunan gargajiya na jihar.
Ayyukan da Tinubu zai kaddamar a Yola
Daga cikin ayyukan da zai ƙaddamar a Yola da Jimeta har da babbar hanyar Galadima Aminu mai layuka takwas wadda ta haɗa Gimba da babban birnin.
Haka zalika, shugaban zai ƙaddamar da wata makaranta wadda ta ƙunshi ajujuwan firamare da sakandare domin inganta harkar ilimi a jihar baki ɗaya.
Sauran ayyukan sun haɗa da sabon babban ɗakin taro, babbar kotun jiha da aka sabunta, sabon rukunin ofisoshin jami'ai, da kuma gidan gwamnati da aka gyara.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar a shafinsa na X ta ce:
"Shugaban zai koma birnin Abuja kai tsaye bayan kammala ƙaddamar da ayyukan da kuma tattaunawa da al'ummar jihar Adamawa a yau."
Kalli bidiyon tafiyar Tinubu a nan kasa:

Source: Twitter
Shettima ya kama hanyar Kano
A gefe guda kuma, bisa umarnin shugaban ƙasa, Mataimakin Shugaba Shettima ya bar Abuja zuwa Kano tare da wata babbar tawagar gwamnatin tarayya baki ɗaya.
Mai magana da yawun Shettima, Stanley Nkwocha ne ya sanar da hakan a shafinsa na X, inda ya ce mataimakin shugaban kasar zai kai ziyarar jaje ne da kuma bada tallafi ga waɗanda gobarar kasuwar Singer ta shafa.
Sanarwar ta ce:
"Gwamnatin tarayya za ta bayar da tallafin kuɗi domin taimaka wa waɗanda abin ya shafa da kuma sake buɗe kasuwar cikin gaggawa."
Tawagar ta haɗa da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin; da Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, da sauran manyan jami'ai.
Bayan jajen gobarar Singer, an shirya mataimakin shugaban kasar zai karɓi Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, zuwa cikin jam'iyyar APC bayan sanarwar ficewarsa daga NNPP.
Kalli bidiyon tafiyar Shettima a nan kasa:
Tinubu ya bada umarni kan gobarar Kano
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya yi alhini game da abin bakin ciki da ya faru a Kano a jiya Asabar 14 ga watan Fabrairun 2026.
Domin nuna tsantsar damuwarsa, Tinubu ya umarci a gudanar da cikakken bincike kan yawaitar gobarar da ke tashi a Kasuwar Singer da ke Kano.
Shugaban ya bada wannan umarni ne bayan gobarar da ta tashi a ranar Asabar ta ci gaba har zuwa safiyar Lahadi, inda ta jawo asara mai yawa ga ’yan kasuwa.
Asali: Legit.ng


