Izala: Sheikh Bala Lau Ya Tura Malamai 2,250 Tafsirin Ramadan 2026

Izala: Sheikh Bala Lau Ya Tura Malamai 2,250 Tafsirin Ramadan 2026

  • Kungiyar Izala karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau ta tura malamai jihohi da kasashe tafsirin watan Ramadan na 2026
  • Hakan na zuwa ne yayin da ke shirin fara azumin watan Ramadan tsakanin ranar Laraba 18 ga Fabrairun 2026 ko Alhamis 19 ga wata
  • Kungiyar Izala ta sanar da cewa Sheikh Usman Isa Taliya ne zai jagoranci tafsir a masallacin Juma'a da ke Filin Kwallo, Bolari, Gombe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Kungiyar Izala da Sheikh Abdullahi Bala Lau ke jagoranta ta tura malamai 2,250 zuwa jihohi da kasashen wajen tafsiri.

Izala ta sanar da haka ne bayan kammala bitar malamai masu tafsiri da ta gudanar a jihar Kaduna a shirin azumin shekarar 2026.

Sheikh Abdullahi Bala Lau a masallaci
Sheikh Bala Lau yayin wani karatu a masallaci. Hoto: Abdullahi Bala Lau
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanai game da tura malamai da kungiyar Izala ta yi ne a wani sako da shafin Jibwis Nigeria ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Ramadan: Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa kan duba wata da ranar fara azumi

Wasu malaman da aka tura tafsiri

1. Sheikh Abdullahi Bala Lau, Jimeta, Jihar Adamawa

2. Sheikh Usman Isa Taliyawa, Masallacin Bolari,Gombe.

3. Sheikh Abbas Muhammad Jega, Birnin Kebbi, Jihar Kebbi.

4. Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, Jalingo, Jihar Taraba.

5. Sheikh Ibrahim Sabi'u Jibia, Jibia, Jihar katsina

6. Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, Jihar Katsina.

7. Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, Masallacin JIBWIS na ƙasa, Utako, FCT Abuja

8. Sheikh Dr Ahmad Abubakar Gumi, masallacin Sultan Bello, Kaduna

9. Sheikh Dr Isma'il Kumo, Masallacin 'Yan Lilo Jihar Kaduna

10. Sheikh Dr Abdulƙadir Saleh Kazaure, Masjidu khadi Muhammad Sambo, Minna, Jihar Niger.

11. Sheikh Abdussalam Abubakar, Baban Gwale, Sokoto Jihar Sokoto.

12. Sheikh Muhammad Sani Adarawa, Bukur, Jihar Plateau

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, kungiyar Izala bata saki sunaye da wuraren da sauran malaman da ta ce ta tura tafsiri ba.

Sheikh Abdullahi Bala Lau
Sheikh Bala Lau yana tafsiri a masallaci. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Malamai sun fara shirin tafsir

Kara karanta wannan

An saka sunan mahaifiyar Tinubu da Fasto ya gina makeken masallaci, ya sha yabo

Malamai sun fara shirye-shirye domin fara gudanar da tafsiri a Ramadan na shekarar 2026 da ke shirin farawa a ranar Laraba ko Alhamis.

Shugaban Izala na jihar Bauchi, Dr Zubairu Abubakar Madaki ya fara kira ga jama'a wajen bayyana yadda za su samu tafsirinsa na bana a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A yau Litinin, 16 ga Fabrairun 2026 shugaban malaman Izala mai hedkwata a Jos, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir zai fara tafsir a jihar Filato.

Ibrahim Maina Muhammad ya wallafa a Facebook cewa:

"Ranar Litinin, 28 ga Sha’aban 1447H, ake sa ran shugaban Majalisar Malamai ta Ƙasa, Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir (Hafizahullah), zai buɗe tafsirin bana a Unguwar Layin Zana, a Masallacin Alhaji Sulaiman Jebu, Jos.
"Muna roƙon Allah ya sanya a buɗe wannan Tafsiri cikin nasara da albarka. Amin."

Za a fara duba watan Ramadan

A wani labarin, kun ji cewa mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi kira ga al'umma da su fara duba watan Ramadan a ranar Talata, 17 ga Fabrairu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga gidan limamin masallacin Izala da dare, sun sace iyalansa

Sanarwar Sarkin Musulmi ya bayyana cewa ana sa ran fara azumin 2026 a ranar Laraba ko Alhamis, gwargwadon yadda aka ga wata.

Ya kuma bayyana halin da Musulmai suka samu kansu a ciki a Najeriya da kasashen duniya, ciki har da kin jinin Musulmai da ya karu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng