Barau Ya Bude Kofar Bada Tallafi, Ya Mika N100m ga 'Yan Kauwar Singer
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau I Jibrin ya bayyana takaici a kan gobarar da ta kwana kusan uku tana ci a Kano
- Sanata Barau ya ziyarci kasuwar domin taya al'umma jajae, musamman yan kasuwan da suak rasa miliyoyin Naira a gobarar
- Gobarar da ta tashi a ranar Asabar, 14 ga watan Fabrairu ta kwana zuwa Lahadi da safiyar Litinin tana ci a wasu sassan kasuwar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ziyarci kasuwar Singer a ranar Lahadi, 15 ga watan 2026.
Sanatan ya bayar da tallafin kudi har Naira miliyan 100 ga ‘yan kasuwar da gobara ta shafa a kasuwar Singer da ke karamar hukumar Fagge a jihar Kano.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Ismail Mudashir, ya fitar.
Sanata Barau ya ziyarci kasuwar Singer
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Sanatan ya bayyana cewa ba yan kasuwa kawai gobarar ta shafa ba, har ma da daukacin al’ummar Kano da ma kasa baki daya.
Ya ce gobarar ta lalata kayayyaki da dukiyoyi da kimarsu ta haura N5bn, lamarin da ya jefa dubunnan iyalai cikin halin kunci.
A cewarsa, kasuwanci shi ne ginshikin rayuwar al’ummar Kano, don haka asarar da aka yi ta taba kowa da kowa.

Source: Original
Sanata Barau ya ce:
"Wannan gobara da asarar da aka yi ta shafe mu duka. Hakika ta shafi daukacin mutanen Kano da ma kasa baki daya. Kasuwanci shi ne jigon rayuwarmu a Kano, don haka wannan lamari ya taba mu kwarai.”
Ya kuma yi alkawarin ganin an samar da na’urar zamani ta dakile gobara a kasuwar domin rage yiyuwar sake faruwar irin wannan iftila’i a nan gaba.
Halin da yan kasuwar Singer ke ciki
A ziyarar da ya kai kasuwar, Shugaban kasuwar Singer, Alhaji Junaidu Zakari, tare da dubunnan ‘yan kasuwar da abin ya shafa, sun tarbi Sanatan.
A nan ne Barau I Jibrin ya mika tallafin Naira miliyan 100 domin rage radadin asarar da aka yi ko za a samu sauki.
Junaidu Zakari ya bayyana cewa kasuwar ta fuskanci manyan gobara biyu a baya-bayan nan, wadanda suka janyo asarar fiye da N5bn.
Ya gode wa Sanatan bisa ziyarar da tallafin da ya bayar, yana mai cewa:
“Muna alfahari da kai a Kano. Muna godiya da dukkanin goyon bayan da kake ba mu. Ka yi mana abubuwa da dama. Mun gode kwarai.”
Asali: Legit.ng

