An Fadi Ranar da ake Hasashe za a Dawo da Zaben 2027 bayan Korafin Musulmai
- A gobe Talata, 17 ga Fabrairu, 2026 majalisar kasa za ta yi zaman gaggawa kan batun saka ranar zaben 2027 a watan Ramadan
- Rahotanni sun nuna cewa majalisar za ta iya dawo da ranar zaben baya domin saukakawa Musulmai bayan korafi da aka rika yi
- Al'ummar Musulmi a fadin Najeriya sun bukaci hukumar zabe ta kasa ta gaggauta sauya ranar a korafe-korafe da suka mika
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar kasa ta sanar da cewa za ta yi zaman gaggawa a ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026, inda ta katse hutunta, yayin da alamu ke nuna cewa ’yan majalisar na iya sake nazari kan ranar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
A cikin wata sanarwa da magatakardan majalisar, Kamoru Ogunlana, ya sanya wa hannu, an umarci Sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai su halarci zama da ƙarfe 11:00 na safe.

Kara karanta wannan
Tuna baya: Yadda INEC ta sauya ranar zaɓe a 2003 bayan korafin Kiristoci a Najeriya

Source: Facebook
Majalisar tarayya za ta yi zaman gaggawa
Jaridar Punch ta wallafa cewa sanarwar gayyatar 'yan majalisar zuwa zaman gaggawa ta ce:
“An umarce ni in sanar da dukkan Sanatoci da Mambobin Majalisar Ƙasa cewa Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai za su koma zaman su da ƙarfe 11:00 na safe a ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026.
“Saboda haka, ana roƙon dukkan Manyan Sanatoci da Mambobi su lura tare da sake tsara shirye-shiryensu domin halartar zaman, domin za a dauki muhimman matakai a kowane zaure a yayin zaman,”
Inji Ogunlana, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Sabuwar ranar zabe a Najeriya?
Wasu majiyoyi daga majalisar, waɗanda suka yi magana bisa sharadin ɓoye sunansu, sun bayyana cewa ba a bayyana wasu batutuwa ba a sanarwar.
Wani Sanata ya ce:
“Wannan zaman na musamman ne domin sake duba ranar zaɓen shugaban ƙasa na 2027 kamar yadda ke cikin gyaran Dokar Zaɓe. Wannan ne ya sa aka katse hutunmu ta hanyar sanarwar da magatakarda ya fitar,”
“Babban burin shi ne a ba da cikakken goyon bayan doka ga buƙatar INEC domin magance damuwar da aka nuna kan zaɓen 2027 da aka tsara a lokacin Ramadan,”
Wani daga cikin 'yan majalisar dattawa ya shaida cewa:
“Idan komai ya tafi yadda aka tsara, za a iya matsar da ranar zaɓen shugaban ƙasa zuwa 13 ga Fabrairu daga 20 ga Fabrairu da INEC ta sanar a baya.”

Source: Facebook
Wannan lamari ya biyo bayan mako guda da Majalisar Dattawa, bayan matsin lambar jama’a, ta amince da tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo.
Yayin da INEC ta ke kokarin kawo shawarar maida zaben ya kasance kusan maki guda kafin azumi, nauyin tsaida ranar zabe yana kan hukumar INEC.
Korafi kan saka zabe a Ramadan
A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon mai taimaka wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya bukaci INEC ta sake duba ranakun zaben 2027.
Ya rubuta cewa idan manufar ita ce a ƙarfafa ba da damar zabe, shirya zabe a Ramadan na iya kawo ƙalubale ga al'ummar Musulmi.
Bashir Ahmad ya kara da cewa dukkan Musulmi a duniya kan rage harkokin duniya a wannan lokaci domin maida hankali kan ibada.
Asali: Legit.ng
