Ramadan: Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa kan Duba Wata da Ranar Fara Azumi

Ramadan: Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa kan Duba Wata da Ranar Fara Azumi

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya fitar da sanarwa game da duba watan Ramadan na shekarar 2026
  • Sanarwar Sarkin Musulmi ta yi magana kan abin da ta kira adawa da al'ummar Musulmi da ta ce an fara a Najeriya a baya bayan nan
  • Majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta yi Allah wadai da kisan Musulmi da aka yi a jihar Kwara, inda aka kashe mutum kusan 200

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta fitar da sanarwa game da duba watan Ramadan na 2026.

Sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Kara karanta wannan

An fadi ranar da ake hasashe za a dawo da zaben 2027 bayan korafin Musulmai

Ami alfarma Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi da wata a sama. Hoto: HQ Nigerian Army|Getty Images
Source: Facebook

Sakatare Janar na NSCIA, Farfesa Is-haq Oloyede ne ya sanya hannu kan sanarwar da majalisar Musulunci ta wallafa a shafinta na X.

Za a duba watan Ramadan a Najeriya

Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana cewa za a fara duba jinjirin watan Ramadan na shekarar 1447/2026 da yammacin ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026.

A cewar sanarwar, idan an ga jinjirin watan a ranar Talata, 17 ga Fabrairu, azumin Ramadan zai fara ne a ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026. Idan kuma ba a gan shi ba, azumi zai fara a ranar Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026.

Leadership ta rahoto ya ce kwamitin duba wata na kasa (NMSC), tare da haɗin gwiwar Hukumar NASRDA sun shirya tsare-tsare domin gudanar da duban watan a hukumance.

Kin jinin Musulmi a Najeriya

Sanarwar ta ce a halin da ake ciki, a bayyane yake cewa shekarar da ta gabata ta kasance mai cike da ƙalubale ga Musulunci da Musulmi a Nijeriya, kamar yadda ta kasance ga miliyoyin Musulmi a faɗin duniya.

Kara karanta wannan

Ramadan: Umarnin da Saudiyya ta ba al'ummar Musulmi game da duba jinjirin wata

Ta ce Musulmi sun tsinci kansu cikin wani yanayin da ake tsananin ƙiyayya ga Musulunci tare da ƙoƙarin danganta su da laifuffuka ta hanyar yaɗa labaran da ba su dace da ainihin halin rashin tsaro da ake ciki a Nijeriya ba.

NSCIA ta ce ajandar wasu masu neman ballewa da wasu shugabannin addini masu tsattsauran ra’ayi ce mayar da Najeriya filin yaƙi inda za a hallaka Musulmi.

Batun kisan Musulmi a Kwara

Majalisar ta yi Allah wadai da mummunan kisan kusan Musulmi 200 a Jihar Kwara wanda ba a ba shi isasshen kulawa a kafafen yaɗa labarai ba.

Wajen da aka kashe Musulmai a Kwara
Yadda aka yi jana'izar Musulmai a Kwara. Hoto: Reuters|BBC
Source: Facebook

Haka kuma ta yi godiya kan yawan ƙorafe-ƙorafen da aka shigar a sakatariyarta bayan sanarwar da hukumar INEC ta fitar cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a watan Ramadan.

Majalisar ta ce wannan sanarwa daga INEC ba ta zo mata da mamaki ba, amma kuma za ta cigaba da sa ido domin lura da yadda za a kaye a karshe.

An bude katafaren masallaci a Kano

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya gina katafaren masallacin da makaranta a jihar.

Kara karanta wannan

Australia: An sanar da ranar da musulamai zasu fara azumin Ramadan na 2026

Mai martaba Aminu Ado Bayero da manyan 'yan siyasa, malaman addini da sauran jama'a sun halarci bude masallacin a unguwar Bachirawa.

Rahoto ya nuna cewa Abdullahi Ganduje ya mika ragamar kula da masallaci da Islamiyyar ga Sheikh Lawal Abubakar Shua'ibu Triumph.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng