Shigo da Guba: DSS za Ta Titsiye El Rufa'i kan Zargin da Ya Yi wa Ribadu
- Alakar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i da Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu na kara tsami
- Ofishin mai ba shugaban shawara kan tsaro (ONSA) ya yi martani game da wata wasika da El-Rufa'i ya rubuta wa Nuhu Ribadu
- A cikin wasikar, tsohon gwamnan Kaduna ya zargi Nuhu Ribadu da shirin shigo da guba Najeriya, yana tambayar dalilin yin hakan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ya mayar da martani ga Malam Nasir El-Rufai da ya nemi karin bayani kan zargin shigo da wani sinadari mai guba daga ƙasar Poland.
A cikin wasiƙar da ya aike wa Nuhu Ribadu, El-Rufai ya ce bayanan da ke hannun shugabannin adawa sun nuna cewa an sayo kimanin kilo 10 na sinadarin Thallium Sulphate ta hannun ONSA.

Kara karanta wannan
Ana zargin an shigo da sinadari mai hadari Najeriya, El Rufai ya aika wasika ga Ribadu

Source: Facebook
Tambayar Nasir El-Rufa'i ga Nuhu Ribadu
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Nasir El-Rufa'i ya nemi karin bayani ne saboda ikirarin cewa sinadarin yana dauke da guba sosai.
A wasikar, da ya wallafa a shafinsa na Facebook, El-Rufa'i ya ce:
“Da yake thallium sinadari ne mai matuƙar guba kuma ana sa ido sosai a kansa, ina ganin yana da muhimmanci, domin kare lafiyar jama’a, tabbatar da gaskiya da kuma ɗorewar amincewar jama’a a yi bayani."
Ya bukaci a yi bayani kan manufar shigo da sinadarin da kuma yadda za a yi amfani da shi, sunan kamfanin da ya samar da shi, da kuma ko an shigo da shi ne bisa izini da sauransu.
Martanin Nuhu Ribadu ga El-Rufa'i
Sai dai a cikin martanin da The Cable ta wallafa, ofishin na ONSA ya musanta zargin tare da buƙatar El-Rufai ya miƙa duk wata shaida da yake da ita ga DSS domin cikakken bincike.
Wasiƙar da Birgediya Janar OM Adesuyi ya rubuta a madadin NSA ta ce:
“Na samu umarni in miƙa gaisuwar mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro tare da tabbatar da karɓar wasiƙar mai girma (Nasir El-Rufa'i) da aka samu a ranar 11 ga Fabrairu, 2026"
Bayan karyata zargin, wasikar ta cigaba da cewa:
“Duk da haka, an miƙa wannan zargi ga hukumar DSS domin gudanar da cikakken bincike.
"Za a gayyace ka da sauran waɗanda ke da alaƙa da lamarin, idan suna da wani bayani, domin su gabatar da shaidar da za ta taimaka wajen bincike mai zurfi, tabbatar da gaskiya da kuma bin doka.”

Source: Facebook
El-Rufa'i ya ce za su kifar da APC
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya ce suna shirye wajen tunkarar jam'iyyar APC a 2027.
Ya bayyana haka ne bayan dawowa Najeriya daga kasar Misra, inda ya ce 'yan APC sun fi so ya zauna a can maimakon ya dawo gida.
El-Rufa'i ya kara da cewa da shi aka kafa gwamnatin Bola Tinubu kuma zai biya bashin kafa gwamnatin wajen kifar da ita a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng
