Gwamna Ya Ware Naira Biliyan 1, Zai Ciyar da Talakawa Abinci a Watan Ramadan
- Gwamnatin Jihar Sokoto ta ware Naira biliyan daya domin ciyar da masu azumi a Ramadan na shekarar 2026 da muke ciki
- Gwamna Ahmed Aliyu ya kaddamar da shirin a Hukumar Tarihi ta jihar, yana cewa an kara cibiyoyin ciyarwa daga 155 zuwa 170
- Shirin, wanda aka fara tun zamanin tsohon gwamna Aliyu Wamakko, na ci gaba da tallafa wa dubban mabukata domin rage radadin talauci
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Sokoto - Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da ware Naira biliyan daya saboda talakawa a azumin Ramadan.
Gwamnan ya dauki matakin ne domin aiwatar da Shirin Ciyarwar Ramadan na shekarar 2026 da muke ciki a yanzu.

Source: Twitter
Yawan mutane da za a ciyar a Sokoto
Rahoton Punch ya ce an shirya raba faranti 34,000 na abinci a kullum ga mabukata a fadin jihar da ke Arewacin Najeriya.
Gwamna Ahmed Aliyu ya kaddamar da shirin a ranar Lahadi a Hukumar Tarihi da ke Sakkwato, yana bayyana shi a matsayin muhimmin tallafin jin kai domin saukaka wa Musulmi masu azumi a watan Ramadan.
Ya ce an kara yawan cibiyoyin ciyarwa daga 155 zuwa 170 sakamakon bukatar jama’a, inda kowace cibiya za ta rika daukar kimanin mutane 200 a lokaci guda domin cin gajiyar shirin.
Ya ce:
“Ina tabbatar muku cewa abincin zai kasance mai tsafta, an shirya shi da kyau kuma mai inganci. Mun dauki ma’aikatan wucin gadi domin tabbatar da tafiyar da shirin cikin nasara."
Gwamnan ya bayyana cewa shirin na daga cikin kokarin gwamnatinsa na bunkasa darajojin Musulunci da jin dadin al’umma, ciki har da gyaran masallatai da makarantu da kuma biyan alawus na wata-wata ga masallatan Juma’a.
Ya kuma yi kira ga kungiyoyin addini, masu hannu da shuni da sauran jama’a da su mara wa gwamnati baya wajen tallafa wa marasa karfi, yana jaddada muhimmancin hadin kai domin tabbatar da babu mai kwana da yunwa a Ramadan.
Gwamnan ya tunatar da cewa an fara shirin ne shekaru 19 da suka gabata a lokacin mulkin tsohon gwamna Aliyu Wamakko, kuma tun daga lokacin yake ci gaba da tallafa wa dubban mazauna jihar.

Source: Facebook
An shawarci kwamitin raba abinci a Sokoto
Shugaban Kwamitin Ciyarwar Ramadan, Aliyu Attahiru, ya ce an kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da gaskiya da ingantaccen gudanarwa, yayin da Kwamishinan Harkokin Addini, Jabir Sani Maihulla, ya bukaci mambobi su yi aiki da gaskiya da tsoron Allah.
Wakilin Sarkin Musulmi, Malam Boyi, ya yaba wa gwamnan kan jajircewarsa wajen tallafa wa jama’a tare da tabbatar masa da goyon bayan masarauta da addu’o’i na alheri.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ‘yan majalisa, sarakunan gargajiya, malamai da shugabannin al’umma, inda aka raba kayan abinci ga cibiyoyi daban-daban domin fara aiwatar da shirin Ramadan na 2026 a hukumance.
Gwamna zai biya albashi saboda Ramadan
Kun ji cewa Gwamna Ahmed Aliyu ya amince da fara biyan albashin Fabrairu daga 13 ga wata domin fara azumin Ramadan.
Gwamnan ya ce hakan zai ba ma’aikata damar shiga Ramadan cikin walwala ba tare da kunci ba.
Biyan albashin ya shafi ma’aikatan jiha, kananan hukumomi, da masu karɓar fansho a duk fadin Jihar Sokoto.
Asali: Legit.ng

