Ana Zargin an Shigo da Sinadari Mai Hadari Najeriya, El Rufai Ya Aika Wasika ga Ribadu

Ana Zargin an Shigo da Sinadari Mai Hadari Najeriya, El Rufai Ya Aika Wasika ga Ribadu

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bukaci karin haske kan wasu sinadarai da aka shiga da su Najeriya
  • El-Rufai ya nemi Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro ya fayyace batun sayen sinadarin 'thallium sulphate' mai matuƙar guba.
  • A wasiƙar da ya aika wa NSA a Abuja, ya nemi bayani kan dalilin shigo da kilo 10 daga Poland, tare da matakan kariya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kaduna - Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nuna damuwa kan zargin shigo da sinadarin guba Najeriya.

El-Rufai ya buƙaci Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro ya yi karin haske kan bayanan da ke yawo kan sayen wani sinadari mai guba.

El-Rufai ya na zargin Ribadu kan shigo da sanadarin guba Najeriya
Malam Nuhu Ribadu da Nasir El-Rufai. Hoto: Nuhu Ribadu, Nasir El-Rufai.
Source: Twitter

Sinadari: El-Rufai ya kalubalanci Ribadu

Hakan na cikin wasiƙar da aka kwanan wata 30 ga Janairu, 2026 wanda ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ganduje ya yi magana kan batan Dadiyata, ya maida martani ga El Rufai

El-Rufai ya ce yana neman “ƙarin haske da tabbaci” kan shirin sayen thallium sulphate daga wata kamfani a Poland.

Ya bayyana cewa gishirin thallium sinadari ne mai matuƙar haɗari kuma ana kula da shi sosai, don haka ya kamata a samu cikakken bayani.

El-Rufai ya lissafo abubuwa shida da yake son a fayyace, ciki har da dalilin amfani, wanda ya sayar, da izinin shigo da kaya.

Haka kuma ya tambayi yawan sinadarin, ƙarfinsa, yadda za a adana shi, da irin kulawar hukumomin lafiya kamar NAFDAC da NCDC.

El-Rufai ya kalubalanci Ribadu kan zargin shigo da guba
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai. Hoto: Nasir El-Rufai.
Source: Twitter

Abin da El-Rufai ke don sani

El-Rufai ya kuma nemi a bayyana ko an yi nazarin haɗarin lafiyar jama’a da kuma matakan rage illa, la’akari da tsananin gubarsa.

Ya jaddada cewa buƙatarsa ba don wata manufa ta ɓoye ba ce, illa don tabbatar da bin doka da ƙa’idoji.

Tsohon gwamnan ya ce amincewar jama’a ga hukumomin ƙasa na ƙaruwa ne idan ana buɗe gaskiya kan lamurra masu haɗari.

Ya ƙara da cewa zai yi maraba da amsa ko wanda zai ci gaba da tattaunawa daga ofishin NSA.

Kara karanta wannan

"Ƙila don ya ƙi APC ne": El Rufa'i ya yi tir da kai sunan Kwankwaso majalisar Amurka

Domin cikawa, ya aika kwafen wasiƙar ga NAFDAC da Hukumar NCDC saboda rawar da suke takawa a fannin tsaron lafiyar jama’a.

Rahotanni sun nuna cewa wannan lamari ya zo ne bayan yunƙurin kama shi a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe.

A wata hira da yan jaridu, El-Rufai ya zargi NSA da bada umarnin kama shi, zargin da ba a tabbatar ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ofishin NSA bai fitar da wata sanarwa a hukumance kan wasiƙar ba.

El-Rufai ya ce ana shirin kashe shi

Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi ikirarin cewa sun saurari wayar mai ba shugaban kasa shawara kan taaro, Nuhu Ribadu.

El-Rufai ya yi zargin cewa Nuhu Ribadu da kansa ya ba da umarnin a kama shi a tsare shi idan ya dawo Najeriya daga kasar waje.

Hadimin shugaban kasa ya nuna damuwa kan kalaman Malam El-Rufai, yana mai cewa ya san abin da suka yi ya sabawa dokar kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com