Yan bindiga Sun Shiga Gidan Limamin Masallacin IZALA da Dare, Sun Sace Iyalansa
- Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai mummunan hari gidan Limamin JIBWIS, Imam Abubakar Muhammad Digare, inda suka yi garkuwa da iyalansa
- Rahotanni sun ce maharan sun kutsa gidan cikin dare, suka kwashe matansa da ’ya’yansa zuwa wurin da ba a sani ba, lamarin ya girgiza al’umma
- An kai harin ne a garin Digare, gundumar Gwana, karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi, inda jama’a ke nuna damuwa kan matsalar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Alkaleri, Bauchi - Al'umma sun shiga tashin hankali bayan kai hari a gidan wani limamin masallacin izala na JIBWIS a jihar Bauchi.
Wani mummunan al’amari ya faru a daren jiya Asabar 14 ga watan Fabrairun 2026 a garin Digare da jihar Bauchi.

Source: Original
Rahoton Bakatsine da ke kawo bayanai game da tsaro a Najeriya ya tabbatar da haka a shafin X da safiyar yau Lahadi 15 ga watan Fabrairun 2026.
An mama wani dan bindiga a Bauchi
Ko a watan Nuwambar 2025, jami’an DSS sun gudanar da samame a kauyen Bojinji, inda suka kama wani ɗan bindiga tare da kwato makamai da miliyoyin Naira.
Bincike ya nuna cewa wanda ake zargi ya koma Bauchi daga Jihar Zamfara yana ikirarin tserewa rikici tare da neman mafaka.
Biyo bayan kama shi, hukumomi sun yi kira ga jama’a su rika kai rahoton mutanen da ba a yarda da halayensu ba, musamman baki.
Yan bindiga sun kai hari gidan limamin izala
Ana zargin wasu ’yan bindiga ne suka kai hari gidan Imam Abubakar Muhammad Digare, babban limamin JIBWIS a garin Digare.
Maharan sun shiga gidan ne cikin duhu, inda suka yi awon gaba da mutane da dama ciki har da matansa da ’ya’yansa, suka tafi da su wurin da ba a sani ba.
Wannan lamari mai tayar da hankali ya jefa tsoro cikin al’ummar Musulmi a yankin, tare da kara nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro da ake fama da ita.

Source: Facebook
Kiran da mutane ke yi hukumomi
An kai harin ne a garin Digare da ke gundumar Gwana, cikin karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi, inda hare-haren garkuwa ke yawaita.
Yayin da al’umma ke kokarin shawo kan hare-hare da garkuwa da mutane, da dama na tambayar yaushe za a kawo karshen wadannan ta’addanci.
Mutane da dama na kira ga hukumomi da su dauki mataki cikin gaggawa domin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi Musulmi da ’yan Najeriya baki daya.
Yan bindiga sun dasa bam a Zamfara
A baya, mun ba ku labarin cewa ana zargin 'yan bindiga sun dasa bam a titin Danjibga zuwa Kuncin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa an gano bam din kuma jami'an tsaro sun yi nasarar kwance shi.
Mai magana da yawun rundunar, Yazid Abubakar ya ce jami'an sashen kwance bam sun tsaftace hanyar, sun tabbatar babu wata barazana.
Asali: Legit.ng

