Bidiyo: Yadda Gobara Ke Cinye Kasuwar Singer, Gwamna Abba Ya Nemi Taimakon Tinubu
- Gwamna Abba Yusuf ya bukaci gwamnatin tarayya ta samar da jiragen sama na kashe gobara biyo bayan tashin gobara a kasuwar Singer
- Gwamnan na jihar Kano ya jinjina wa kokarin ma'aikatan kashe gobara yayin da ya ziyarci kasuwar da ta babbake a ranar Asabar
- Abba Yusuf ya yi kira ga yan kasuwa da su kwantar da hankulansu tare da baiwa jami'an agaji cikakken hadin kai domin shawo kan wutar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - A ranar Asabar, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta samar da kayan kashe gobara na zamani a ƙasar.
Gwamnan ya buƙaci a samar da tallafin jiragen sama masu kashe gobara da sauran muhimman kayayyaki biyo bayan gobara ta biyu da ta tashi a kasuwar Singer.

Kara karanta wannan
Aminu Vs Sanusi II: Gwamna Abba ya sake tabo batun rikicin sarautar Kano a gaban Sanata Barau

Source: Facebook
Gwamna Abba ya nemi taimakon Tinubu
Abba Yusuf ya yi wannan kiran ne lokacin da ya isa sashen Gidan Gilas na kasuwar, yayin da gobarar ke ci gaba da lallata shaguna da dukiya, in ji sanarwar Sanusi Bature Dawakin Tofa a shafinsa na Facebook.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan ya fitar, Abba Yusuf ya sanar da daukacin jama'ar jihar Kano halin da ake ciki game da gobarar kasuwar.
Sunusi Bature ya ce:
"Gwamna Yusuf ya bukaci gwamnatin tarayya ta shigo ciki domin samar da kayan aiki na zamani gami da tallafin jiragen sama domin shawo kan gobarar.
"Wannan matakin zai taimaka wajen dakile afkuwar irin wannan annoba a nan gaba da kuma kare dukiyoyin dake cikin manyan kasuwanninmu na jihar Kano."
Gwamna Yusuf ya lura cewa irin wannan tallafin zai ƙarfafa gwiwar ma'aikatan kashe gobara wajen mayar da martani cikin gaggawa a manyan cibiyoyin kasuwanci na ƙasar.
Muhimmancin tallafi ga ma'aikatan agaji
Sanarwar ta rahoto Gwamna Abba Yusuf yana cewa:
"Wannan tallafin zai taimaka matuka wajen inganta ayyukan ma'aikatanmu da kuma rage asarar da ake samu yayin da irin wannan mummunan lamari ya faru."
Gwamnan ya jinjina wa ƙoƙarin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano da sauran hukumomin tsaro bisa jajircewar da suka nuna wajen yaƙar wannan gagarumar gobara.
Haka zalika, gwamnan ya yi kira ga ƴan kasuwa da mazauna yankin da su kwantar da hankulansu tare da ba wa ma'aikatan agaji haɗin kai yadda ya kamata, in ji rahoton Punch.
"Muna rokon yan kasuwa da mazauna yankin da su tallafawa jami'an agaji dake aiki dare da rana domin kashe wutar da kare rayuka," in ji Abba Yusuf.

Source: Facebook
Tarihin gobara a kasuwar Singer
Kasuwar Singer tana ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a Kano, kuma wannan lamari shi ne gobara ta biyu da aka samu a cikin ginin kasuwar.
Rahotanni sun nuna cewa wannan gobarar ta laƙume dukiya ta biliyoyin nairori, wanda hakan ya jefa ƴan kasuwa da dama cikin halin damuwa da kuma fargabar rasa sana'arsu.
Gwamnati ta yi alƙawarin gudanar da bincike na tsanaki domin gano asalin abin da ya haddasa gobarar da kuma samar da hanyoyin kariya daga sake afkuwar hakan.
A halin yanzu, jami'an kashe gobara suna ci gaba da kokarin tabbatar da cewa wutar ba ta shafi sauran sassan kasuwar ba domin rage asarar dukiya.
Gidan rediyon Dala FM ya wallafa bidiyon gobarar a shafinsa na Facebook. Kalli bidiyon a kasa:
"Mun rasa sama da N30m" - Dan kasuwa
Wani dan kasuwar Singer, Nazifi Adam Isa da wakilin Legit Hausa ta zanta da shi, ya ce sun tafka asara mai yawa, inda shagonsa da na mahaifinsa suka kone kurmus.
Nazifi Isa ya ce:
"Akwai shagona, akwai na mahaifinmu wanda muke ciki, sun kone. Akalla baburan da suka kone a iya jiya da daddare sun kai 200, kekuna ma za su kai 200.
"Dole shi Musulmi zai dauki kaddara a duk yadda tazo masa, amma gaskiya mun ji ba dadi sosai, saboda yanayin yadda 'yan uwa suka shiga alhini marar misaltuwa.
"Mun rasa sama da Naira miliyan 30 a wannan gobara."
Gobara ta sake tashi a kasuwar Singer
Tun da fari, mun ruwaito cewa, a karo na biyu cikin kasa da makonni biyu, kasuwar Singa da ke cikin jihar Kano ta sake fuskantar ibtila'in gobara ranar Asabar.
Rahotanni daga yan kasuwa sun nuna cewa gobarar ta kama ne a sashen Gidan Glass da misalin karfe 4:00 na yamma.
Babu wata sanarwa a hukumance kawo yanzu amma majiyoyi sun tabbatar da cewa motar 'yan kwana-kwada daya kacal ta ka dauki kasuwar.
Asali: Legit.ng


