Shehin Malami Ya Yi wa Naja’atu Wankin Babban Bargo kan Taba Sheikh Pantami
- Wani malamin Musulunci a Zaria ya soki ‘yar siyasa, Naja'atu Mohammed kan kalaman da ta yi game da Sheikh Isa Ali Pantami
- Malamin ya kare Pantami, ya ce duk da kura-kurai, alherinsa da gudunmawarsa ga addini da al’umma sun fi yawa a mizanin adalci
- Ya kuma bukaci malamai su shiga siyasa domin kawo sauyi a kasa, yana mai cewa bai kamata su ji tsoron sukar wasu ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Zaria, Kaduna - Malamin Musulunci a Najeriya, Ustaz Alkali Abubakar Salihu Zaria ya yi magana kan siyasar Sheikh Isa Ali Pantami.
Sheikh Alkali Salihu Zaria ya kuma caccaki yar siyasa a Kano, Naja'atu Mohammaed game da taba Malam Isa Pantami da ta yi game da siyasa.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano wannan martani ne a wani bidiyo da mai amfani da shafin X, @el_uthmaan ya wallafa a jiya Asabar 14 ga watan Faburairun 2026.
Alkali Abubakar Salihu Zaria ya soki Naja'atu
A cikin bidiyon, malamin ya nuna takaici game da kalaman Naja'atu kan Malam wanda ya ce cin mutuncin addini ne da malanta.
Ya ja kunnen Naja'atu duba da cewa ba ta taba fadin alherin Malam Isa Pantami ba duk da gudunmawar da ya ba al'umma da addini.
Ya ce:
"Akwai wata mata yar siyasa ana kiranta Hajiya Naja'atu, ta zo ta ci mutuncin Malam Isa Ali Pantami, to abin da kika yi, kin yi kuskure.
"Domi wannan abin da kika yi suka ne ga addini, ga Musulunci da kuma malamai da dalibansu, a mizani da adalci, alherin Isa Pantami sun fi kuskurensa yawa.
"Shekara nawa ya yi yana karantarwa da al'umma yana gyara mutane daga zalunci zuwa mutanen kirki daga duhu zuwa haske."

Source: Facebook
Pantami: Shehin yan kalubalanci Naja'atu
Ya kalubalanci Naja da ta bayyana amfanin da ta yi wa al'umma tun bayan fara harkokin siyasa a rayuwarta.
Malamin ya bayyana cewa dole malamai su fito takara domin kawo sauyi a kasa inda ya ce kowace kujera sai malamai sun yi takara.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ganduje ya yi magana kan batan Dadiyata, ya maida martani ga El Rufai
"Babu ranar da kika taba yaba masa, kika fadi alherinsa kuma tun da kika fara siyasar har yau ban ga abin da kika yi wa Musulunci ba.
"Ban ga abin da kika amfanar da kasar ba, ga Musulmi da Kiristoci sai zage-zage da cin mutunci, an aiko ki ne?
"Muna hanya, wannan takarar da malamai za a yi ta, kansiloli malamai, ciyamomi malamai, yan majalisu malamai haka ma gwamnoni malamai sai ki mutu."
- cewar malamin a Kaduna
Ya ce a nan Kaduna ma an samu Sheikh Ahmad Tijjani ya fito takarar gwamna, malam Isa yana daidai yana kuskure duk da alherinsa ya fi yawa.
Ya shawarci malamai su fito takara, ka da maganarta ya hana su, ya ce da maganarta da fitsarin da ya yi bara duk daya uwarsu daya ubansu daya.
Pantami ya ki karbar mukami daga Tinubu
An ji cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya sabunta rajistar zama dan jam'iyyar APC a Gombe inda ya bayyana gaskiyar alakarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Malamin ya bayyana cewa har yanzu yana ba Tinubu shawarwari kuma yana karba saboda kokarinsa a nasarar shugaban kasar a zaben 2023.
Pantami ya kuma fadi dalilin da ya sa bai karbi tayin mukamai uku da Tinubu ya yi masa ba, yayin da ake zargin zai nemi takarar gwamna a 2027.
Asali: Legit.ng
