Kwankwaso Ya Kadu da Tashin Mummunar Gobara a Kano, Ya Tura Sako ga Abba, Tinubu
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna alhini kan sabuwar gobarar da ta tashi a kasuwar Singer da ke Kano a yau Asabar
- Tsohon gwamnan Kano ya aike da sakon jaje ga ‘yan kasuwar da suka yi asara, yana kira da a kawo daukin gaggawa
- Kwankwaso ya roki hukumomi, jami’an tsaro da masu hannu da shuni su hada kai wajen tallafa wa wadanda abin ya shafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nunu kaduwarsa bayan sake samun mummunar gobara a kasuwar Singer.
Tsogon gwamnan Kano ya bayyana takaici kan lamarin inda ya tura sakon jaje ga wadanda suka tafka asara sanadin gobarar.

Source: Facebook
Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin X na jagoran Kwankwasiyya a daren yau Asabar 14 ga watan Faburairun 2026.
Yadda ake yawan samun gobara a Kano
Wannan ba shi ne karon farko ba da ake samun iftila'in gobara a kasuwannin jihar Kano wanda ke jawo asarar duniyoyin miliyoyi.
Ko a makon da ya gabata ma, kasuwar Singer ta kama da wuta wanda daruruwan yan kasuwa suka tafka asara mai tarin yawa.
Abba ya ba yan kasuwar Singer kyautar kudi
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyara kasuwar Singer domin jajanta wa ‘yan kasuwar da gobara ta shafa da ta jawo masu asarar miliyoyi.
Bayan ziyarar da ya kai, Gwamna Abba ya bayyana cewa za a tallafa wa yan kasuwar tare da daukar matakai don kare afkuwar haka a gaba.
Gwamnati ta bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga waɗanda suka yi asara, sannan an sanar da aikin faɗaɗa da gyaran tituna a kasuwar.

Source: Facebook
Sakon Kwankwaso ga yan kasuwar Singer
Kwankwaso ya bayyana takaicinsa game da faruwar lamarin inda ya tura sakon ta'aziyya ga dukkanin wadanda abn ya shafa.
Ya kiraye gwamnatin tarayya da ta Kano da sauran hukumomi da abin ya shafa da su kawo daukin gaggawa da taimako a kasuwar.
Ya ce:
"Ina mika sakon ta’aziyyata ga dukkanin wadanda mummunar gobarar da ke ci gaba da tashi a Kasuwar Singer da ke Kano ta shafa.
"Ina kira gaggawa ga hukumomin gwamnati da abin ya shafa, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta Jihar Kano, jami’an tsaro, kungiyoyin jin kai, masu hannu da shuni da kuma bangaren masu zaman kansu da su gaggauta tashi tsaye su bayar da duk wani tallafi da ya dace; ko kayan kashe gobara ne, taimakon jinya na gaggawa ko kayan agaji, domin shawo kan wannan gobara tare da rage radadin da wadanda abin ya shafa ke ciki."
Peter Obi ya kai ziyara kasuwar Singer
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya kai ziyarar jaje kasuwar Singer a Kano domin nuna alhini ga ’yan kasuwar da mummunar gobara ta shafa.
A cikin bayanin da ya yi, Peter Obi ya bayyana cewa gobarar ta jawo babbar asara ga ’yan kasuwar, jihar Kano da ma tattalin arzikin Nijeriya baki ɗaya.
Bayan ba da gudummuwa da ya yi, Obi ya yaba wa gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso bisa kokarin da suka yi.
Asali: Legit.ng

