'Yan Bindiga 200 Sun Shiga Garuruwa 3 da Asubah, Sun Kashe Mutane Sama da 30
- 'Yan bindiga kusan 200 sun shiga kauyuka uku a yankin karamar hukumar Borgu ta jihar Neja da sanyin safiyar yau Asabar
- Rahotanni daga mazauna yankin sun tabbatar da cewa maharan sun kashe akalla mutane 32, sun kona gidaje kuma sun tafi da wasu zuwa daji
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin, amma ta ce har yanzu ba a gama tattara bayanan barnar da maharan suka yi ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - ’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 32 a jerin hare-hare da suka kai kan garuruwan Tunga-Makeri, Konsoko da Pissa a Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja.
Mazauna yankin sun ce harin farko ya faru ne a ƙauyen Tunga-Makeri da ke mazabar Konkoso da misalin ƙarfe 3:00 na asubahin yau Asabar, inda aka kashe mutum shida.

Source: Original
Majiyoyi sun tabbatarwa Daily Trust cewa daga baya ’yan bindigar sun mamaye ƙauyukan Konsoko da Pissa da misalin ƙarfe 6:00 na safe, suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
'Yan bindiga 200 sun mamayi mutane
A harin, an ruwaito cewa yan bindigar sun kashe mutum 26 tare da ƙona gidajen jama'a da dama, ciki har da ofishin ’yan sanda na yankin.
Majiyoyi sun bayyana cewa har yanzu ba a tantance ainihin adadin waɗanda suka mutu a harin da aka kai ƙauyen Pissa da ke yankin Kabe/Pissa ba.
Wani mazaunin yankin, Hassan Abdullahi, ya shaida wa Vanguard cewa maharan sun kai sama da 200, kuma sun kwashe sa’o’i suna aikata ta’asar.
Ya ce harin na ranar Asabar ya fara da misalin ƙarfe 6:00 na safe kuma ya ɗauki lokaci har zuwa ƙarfe 10:00 na safe.
Ya kuma bayyana cewa ƙauyukan da aka kai wa harin suna da nisan kusan kilomita 200 daga sansanin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da ke New Bussa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Borgu.

Kara karanta wannan
Lamari ya juya: Ƴan bindiga sun yi saɗaf saɗaf sun hallaka 'DPO' bayan sace shanu
Martanin rundunar ’yan sandan Neja
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da cewa harin Tunga-Makeri ya faru da misalin ƙarfe 3:00 na asubahin Asabar.
Ya ce mutum shida sun rasa rayukansu a ƙauyen, an ƙona wasu gidaje, sannan an yi garkuwa da wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba.

Source: Twitter
Abiodun ya kuma tabbatar da cewa ’yan bindigar sun wuce zuwa Konsoko, amma ya ce har yanzu cikakkun bayanai kan harin ba su fito fili ba.
Ya ƙara da cewa an tura jami’an tsaron hadin gwiwa zuwa yankin domin tantance halin da ake ciki, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.
Yan ta'adda sun saki bidiyon mutanen Kwara
A wani rahoton, kun ji cewa wasu yan ta'adda da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun saki bidiyon mutane 176 da suka sace a garin Woro dake jihar Kwara.
Wannan lamari ya faru ne a ƙaramar hukumar Kaiama dake jihar Kwara, inda mutanen garin suka rika kira ga gwamnati da ta gaggauta ceto 'yan uwansu da aka sace.
A cikin bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, an lura cewa mafi yawan waɗanda aka yi garkuwa da su, da suka kai kimanin mutum 176 mata ne da ƙananan yara.
Asali: Legit.ng
