Sauki daga Allah: Farashin Kayan Abinci Ya Ruguzo ana Shirin Ramadan

Sauki daga Allah: Farashin Kayan Abinci Ya Ruguzo ana Shirin Ramadan

  • Bincike ya nuna cewa farashin abinci na cigaba da sauka a wasu sassan jihar Taraba yayin da Ramadan ke kara karatowa a Najeriya
  • 'Yan kasuwa sun nuna damuwa kan yadda kayan da suka noma ba su yin farashi sosai, suna cewa sun kashe kudi sosai wajen noma
  • Farashin shinkafa, wake, gero da wasu kayyakin abinci da ake amfani da su a yau da kullum ne suka kara sauka a kasuwannin jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba - Manoman da suka kawo amfaninsu kasuwar hatsi ta Mutum Biyu a ranar Talata sun yi takaici bayan sun gano cewa farashin kayayyakin gona ya ƙara faɗuwa.

Rahotanni daga kasuwannin Iware da Mutum Biyu sun gano cewa farashin hatsi ya sauka zuwa mafi ƙarancin farashi a cikin shekarun baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Sojan Amurka dan asalin Najeriya ya nutse a teku bayan fadowa a jirgin yaki

Kasuwar da ake sayar da kayan abinci
Yadda ake sayar da kayan abinci a kasuwa. Hoto: Garba Muhammad
Source: Facebook

Ramadan: Farashin abinci ya auka sosai

Binciken Daily Trust ya nuna cewa buhun masara mai nauyin kilo 100 da aka sayar kan N20,000 a makon da ya gabata ya sauka zuwa tsakanin N15,000 da N17,000 a wannan makon.

Haka kuma, buhun rogo mai nauyin kilo 100 da aka sayar kan N8,000 a makon jiya ya sauka zuwa N4,000, yayin da buhun shinkafa mai nauyin kilo 100 da aka sayar kan N24,000 ya sauka zuwa N19,000.

Karin rahotanni sun tabbatar da cewa farashin wake fari, gero, shinkafar gida da aka sarrafa, man ja da dawa ma ya sauka a faɗin jihar.

Manoma sun yi korafin saukar farashi

Bala Dauda Tutare daga karamar hukumar Gassol ya shaida wa manema labarai cewa ya yi takaici kan ci gaba da faɗuwar farashin amfanin gona.

Ya ce manoman da suka noma rogo, masara da dawa a bana su ne suka fi shan wahala da tafka asara saboda rugujewar farashi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sa kayan sojoji, sun sace mata a gidan biki a Kano

Manomin ya bayyana cewa ya zuba Naira miliyan 4 a gonar rogonsa da fatan samun riba, amma bayan girbi, farashin rogo ɗanye da busasshe ya faɗi.

Taswirar jihar Taraba
Taswirar jihar Taraba a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Tutare ya ƙara da cewa farashin buhun rogo busasshe mai kilo 100 yanzu N4,000 ne, kuma yana neman mai saye da zai ɗauki buhuna 3,000 gaba ɗaya ko da a kan N3,000, amma har yanzu bai samu ba.

Korafn wani manomi a Taraba

Wani manomi mai suna Suleiman Muhammed, ya ce ya yi asarar sama da Naira miliyan 3 sakamakon halin da ake ciki na saukar farashi.

Muhammed ya ce jim kaɗan bayan ya girbe shinkafa da masararsa, farashin amfanin gona ya fara faɗuwa. Ya jira ko farashin zai tashi, amma sai ya ci gaba da sauka.

“Sa’a na shi ne kuɗin da na zuba nawa ne; ban karɓi rance ko bashi daga banki kamar yadda wasu manoma suka yi ba,”

Inji shi.

Wani karamin manomi a Garba-Chede, Ƙaramar Hukumar Bali, Silvanus James ya ce yana guduwa a gidansa domin mutanen biyu da ya karɓi bashi a wurinsu suna matsa masa ya biya.

Kara karanta wannan

Hafsun sojoji ya fadi abin da ke jiran wadanda suka kitsa juyin mulki

Legit ta tattauna da manomi

A tattaunawa da Legit, wani manomi a jihar Gombe da ya ce ya yi noman dankali a karamar hukumar Akko ya ce bai tsira daga tafka asara ba.

Ya ce:

"Ni ma na yi asara, sai dai ni ba ta hanyar karyewar farashi ba ne, kayan noman nawa dabbobi suka cinye.
"Mun kama masu shanun domin su biya mu, amma daga baya muka fahimci cewa wai dole sai dai a rage mana asara."

Za a tallafawa manoma a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Ministan kudin Najeriya, Wale Edun ya ce gwamnatin tarayya za ta ba manoma tallafi na musamman.

Edun ya bayyana cewa ya zama dole a tallafa musu lura da yadda farashin kayan abinci ya karye bayan kammala noma a bana.

Ya kara da cewa idan manoma suka cigaba da karyewa za a iya wayan gari mutane da dama sun daina kashe wajen noma a kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng