Daruruwan Mutane da Aka Hallaka Wata 2 bayan Tinubu Ya Sa Dokar Ta Baci kan Tsaro

Daruruwan Mutane da Aka Hallaka Wata 2 bayan Tinubu Ya Sa Dokar Ta Baci kan Tsaro

  • Fiye da mutum 316 sun mutu cikin kwanaki 71 bayan Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro
  • Rahoton ya nuna an kai hare-hare sama da 31 a jihohi 15 tun bayan ayyanawar dokar ta-baci da aka yi
  • A cikin sa’o’i 48 kacal, mutum 114 sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda a sassa daban-daban

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - A ranar 26 ga Nuwamba, 2025, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro a Najeriya.

Matakin ya biyo bayan hare-haren ta’addanci kan wani coci a jihar Kwara da kuma makarantu a jihohin Kebbi da Niger, inda aka sace sama da mutum 350 cikin ‘yan kwanaki kaɗan.

Ana ci gaba da kisan al'umma bayan Tinubu ya sanya dokar ta-baci kan tsaro
Shugaba Bola Tinubu da rundunar sojojin Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Yawan mutane da aka hallaka bayan dokar ta-baci

Shugaban ya bayar da umarnin karin daukar sojoji aiki tare da janye jami’an ‘yan sanda da ke gadin manyan mutane domin a kara karfi a yankunan da suka fi fama da rashin tsaro, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kai wasikar kai hari kauyuka, mutane sun fara gudu

Ya kuma ce za a tura jami’an tsaron daji domin fatattakar ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da ke buya a cikin dazuka.

Legit Hausa ta duba wasu daruruwan mutane da yan bindiga suka hallaka bayan sanya dokar ta-baci kan tsaro.

Fiye da mutum 316 sun mutu cikin watanni 2

Sai dai sama da watanni biyu bayan jawabin shugaban, rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta’addan sun kashe fiye da mutum 316 a jihohi 15.

An kai hare-hare sama da 31 tun daga ranar ayyana dokar ta-ɓaci, inda kusan kowace rana ake samun rahoton kisan gilla.

Wannan adadi kuwa ya ta’allaka ne kan hare-haren da kafafen yada labarai suka ruwaito kacal.

1. Hare-hare a watan Disambar 2025

A farkon watan Disambar 2025, an kashe mutum 28 a jihohin Sokoto, Anambra, Taraba da Zamfara wanda ya tayar da hankulan al'ummar yankunan da abin ya shafa.

Daga bisani, wasu 48 sun mutu a lokacin bukukuwan Kirsimeti a jihohin Plateau, Benue, Borno, Zamfara, Gombe, Adamawa da Nasarawa.

Har ila yau, an samu hare-hare a masallaci da kasuwanni, ciki har da fashewar bam da ya hallaka masu ibada a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Karshen duniya: Ta kwabe wa yaro bayan zargin shi da hannu a garkuwa da mahaifinsa

Tinubu ya ɗauki mataki kan tsaro bayan hare-haren yan bindiga
Ministan tsaro a Najeriya, Christopher Musa da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

2. Kisan mutane 42 a jihar Niger

A ranar 3 ga Janairun 2026, ‘yan bindiga sun kai hari kasuwar Kasuwan Daji a karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.

Yan bindigan sun ci gaba da kai hare-hare a wasu kauyuka na Agwara ba tare da wata turjiya ba har tsawon mako guda wanda ya kara jawo asarar rayukan mutane.

A karshe, an tabbatar da mutuwar akalla mutum 42 tare da sace wasu da dama ciki har da yara, cewar rahoton The Guardian.

3. Mutum 84 sun mutu a Janairun 2026

A watan Janairu kadai, akalla mutum 84 sun mutu a jihohin Plateau, Benue, Oyo, Sokoto, Kano, Borno da Kogi sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da Boko Haram.

Daga ciki har da kisan wata mata da ‘ya’yanta shida a Kano, da kuma harin bam da hare-haren kan ma’aikata a Borno.

An kashe mutane fiye da 300 bayan sanya dokar ta-ɓaci kan tsaro
Karamin ministan tsaro a Najeriya. Hoto: Dr. Bello Matawalle.
Source: Twitter

4. Mutum 114 cikin sa’o’i 48 a jihohi 4

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi kisa yayin da suka sace limami, ladan da wasu mutane

A ranar 2 da 3 ga Fabrairun 2026, akalla mutum 114 sun mutu cikin sa’o’i 48 ba tare da aikata laifin komai ba.

An kashe mutum kusan 200 a karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara, yayin da wasu 13 suka mutu a Katsina, sannan wasu 17 a Borno da 4 a Benue.

Wasu rahotanni daga irinsu Al Jazeera sun ce mutanen da aka hallaka a harin Kaiama sun kai 200.

Rahoton ya nuna cewa duk da ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro, hare-haren ‘yan ta’adda na ci gaba da jefa al’umma cikin alhini a sassa daban-daban na Najeriya.

Harin Kwara ya tayar da kura a Najeriya
Gwamna Abdul Rahman AbdulRazaq na jihar Kwara da Bola Tinubu. Hoto: Kwara State Government, Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Tsaro: An bukaci Tinubu ya sanya dokar ta-baci

A baya, an ji cewa jam’iyyar ADC ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta sanya dokar ta-baci kan matsalolin tsaro musamman a Arewa.

ADC ta ce kashe-kashen al’umma a Malumfashi a Katsina da hare-haren Zamfara na nuni da rushewar tsarin tsaron Najeriya baki ɗaya.

Jam’iyyar ta kuma caccaki shugabannin PDP da suka gudanar da taron siyasa a Zamfara jim kaɗan bayan harin, tana kiran hakan rashin tausayi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.