INEC Ta Fadi Dalilan Sa Zaben 2027 a Ramadan da Matakin da za Ta Dauka

INEC Ta Fadi Dalilan Sa Zaben 2027 a Ramadan da Matakin da za Ta Dauka

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi karin bayani game da saka ranar zabukan da za a yi a Najeriya a shekarar 2027
  • Hakan na zuwa ne bayan jama'a da dama, ciki har da Atiku Abubakar sun yi korafi game da saka ranar zaben a watan Ramadan
  • Rahotanni sun bayyana cewa bayan sauraron korafin al'umma da dama a Najeriya, hukumar INEC ta bayyana matakin da za ta dauka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta yi kan bayani kan korafin jama’a da ya taso sakamakon fitar da jadawalin lokuta da ranakun babban zaɓen 2027.

Al'umma da dama, musamman Musulmi ne suka yi korafi da cewa bai kamata ranar zaben ta dace da lokacin da al'umma ke azumin Ramadan ba.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: An kira zaman gaggawa kan sanya ranakun zaben 2027 a watan Ramadan

Shugaban hukumar INEC a ofis
Shugaban hukumar INEC a ofis. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Dalilin sa ranar zabe a Ramadan

Hukumar ta wallafa a Facebook cewa an tsara jadawalin ne bisa bin ƙa’idojin lokutan da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, dokar zaɓe ta 2022, da ka’idoji da dokokin INEC na gudanar da zaɓe na 2022 suka tanada.

Ta ce ka’idoji da dokokin INEC da aka fara aiwatar da su tun 2019 sun riga sun tsayar da ranakun da za a gudanar da zaɓe. Sashe na 2 na dokar ya tanadi cewa:

“Zaɓen Shugaban Ƙasa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, da kuma na Majalisar Tarayya, za su gudana ne a ranar Asabar ta uku na watan Fabrairu a duk shekarar babban baɓe; yayin da zaɓen gwamna da mataimakin gwamna da na majalisun dokokin jihohi za su gudana makonni biyu (2) bayan haka.”

A kan haka ne INEC ta ce ta tsayar da ranar Asabar, 20 ga Fabrairu 2027 domin zaɓen shugaban kasa da kuma Asabar, 6 ga Maris 2027 domin zaɓen gwamna duk da dacewa da lokacin azumi.

Kara karanta wannan

An gano matsalar da za a iya samu a zaben shugaban kasar 2027 saboda azumin Ramadan

Wani matakin hukumar INEC za ta dauka?

INEC ta ce ta yi la'akari korafin da masu ruwa da tsaki suka bayyana dangane da dacewar waɗannan ranaku da azumin Ramadan na 2027.

Hukumar ta tabbatar wa jama’a cewa za ta kula da duk wani korafi da ka iya shafar halartar mutane zaɓe da kuma yadda za a gudanar da shi gaba ɗaya.

Ta ce tana cigaba da tattaunawa, kuma idan ya zama dole, za ta nemi matakin gyara ta fuskar majalisa domin magance damuwar da aka nuna.

Wasu jami'an huumar INEC
Jami'an INEC a ofis a lokacin saka ranar zaben 2027. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jagoran ADC a Najeriya, Atiku Abubakar na cikin wadanda suka yi korafi a dandalin Facebook.

Legit ta tattauna da Usman Bojude

A tattaunawa da wani matashi a jihar Gombe, Usman Bojude ya bayyanawa Legit Hausa cewa akwai bukatar sauya ranakun zaben 2027.

Ya ce:

"Idan aka ce za a yi zabe a Ramadan mutane da dama ba za su je kada kuri'a ba.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: INEC ta sanar da ranar zaben shugaban kasa da na gwamnoni a 2027

"Jama'a za su tsaya tsare kuri'unsu ne ko kuma buda baki da yamma bayan kada kuri'a?"

INEC za ta yi zabe a 2026

A wani labarin dabam, mun kawo muku cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) za ta gudanar zabe a wasu jihohin Najeriya.

A watan Fabrairun 2026 INEC za ta gudanar da zaben kananan hukumomi a Abuja, da zaben cike gibi a wasu jihohi da suka hada da Kano.

Bayan zabukan cike gibi a jihohi, hukumar INEC za ta gudanar da zaben gwamna a jihohin Osun da Ekiti a shekarar 2026 da muke ciki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng