Lamari Ya Juya: Ƴan Bindiga Sun Yi Saɗaf Saɗaf Sun Hallaka 'DPO' bayan Sace Shanu
- Wani hari da ake zargin na ‘yan bindiga ne ya yi ajalin DPO, CSP Muhammad Sani Sagir, a karamar hukumar Rimi ta jihar Katsina yau Juma’a
- Marigayin da tawagarsa sun je ceto shanu da aka sace, inda suka bi maharan zuwa daji kafin su fada kwanton bauna mai muni
- ‘Yan sanda uku da wata mata sun jikkata, yayin da jami’ai suka fara farautar maharan da suka tsere daga yankin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Wani mummunan al’amari ya faru a unguwar Magaji a jihar Katsina bayan hallaka babban dan sanda.
Lamarin ya faru ne a mazabar Majen-Gobir da ke karamar hukumar Rimi a jihar Katsina da ake fama da hare-haren ta'addanci.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun hallaka DPO a Katsina
Rahoton Bakatsine ya tabbatar da haka a shafin X a yau Juma'a 13 ga watan Faburairun 2026 inda ya ce an kashe DPO, CSP Muhammad Sani Sagir.
'Dan sandan ya rasa ransa ne a wani kwanton bauna da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai da safiyar Juma’a 13 ga watan Fabrairun 2026.
Rahotanni sun ce CSP Sagir da tawagarsa sun amsa kiran gaggawa kan satar shanu da misalin karfe 10:00 na safe wanda lamarin ya jawo asarar ransa.
An ce jami’an sun bi sawun wadanda ake zargi zuwa wani daji da ke kusa domin kwato dabbobin da aka sace, amma sai suka fuskanci ruwan wuta mai tsanani daga maharan.

Source: Original
Munanan raunuka da dan sandan ya samu
Rahotanni sun bayyana cewa DPO din ya samu munanan raunuka a yayin harin, kuma daga bisani ya rasu sakamakon raunukan da ya ji.
Haka kuma, wasu ‘yan sanda uku da wata mata sun jikkata a harin, yayin da maharan suka tsere da karin shanu da sauran dabbobi daga yankin.
Majiyoyin cikin gida sun ce an kashe daya daga cikin ‘yan bindigar a lokacin artabun, sannan an samu nasarar kwato wasu daga cikin dabbobin da aka sace.
Wane hali yan sandan suke ciki yanzu?
An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa wani asibiti da ke kusa domin samun kulawar likitoci, yayin da al’umma ke cikin jimami kan wannan mummunan hari.
A halin yanzu, hukumomi sun kaddamar da farautar maharan da suka tsere, domin kamo su tare da tabbatar da tsaro a yankin da abin ya faru, cewar rahoton Daily Post.
'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro a Katsina
A baya, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan jami'an tsaro na Rundunar Community Watch Corps (C-Watch) a jihar Katsina.
Tsagerun 'yan bindigan sun shirya kwanton bauna ne dai ga jami'an tsaron lokacin da suke kan hanyar tafiya zuwa wani kauye domin ci gaba da kare rayukan al'umma.
An kashe jami'in tsaro tare da jikkata wani daban yayin artabun da aka yi a kan hanyar zuwa wani kauye da ke karamar hukumar Musawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

