An Gano Matsalar da Za a Iya Samu a Zaben Shugaban Kasar 2027 saboda Azumin Ramadan
- Tsohon hadimin shigaban kasa, Bashir Ahmad ya lura da matsalar da za a iya samu a zaben 2027 saboda musulmai na azumin Ramadan
- A yau Juma'a, INEC ta sanar da ranakun da za ta gudanar da zaben shugaban kasa, gwamnoni da yan majalisar tarayya da na jihohi
- Bashir Ahmad ya bukaci Hukumar INEC ta sake duba wadannan ranaku da ta sanya aaboda duka za su fado ne a watan Ramadan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin midiya, Bashir Ahmad, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sake duba ranakun zaɓen 2027.
Bashir Ahmad, wanda ya yi aiki a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, ya ce jadawalin ya zo daidai da watan azumin Ramadan, wanda hakan na iya shafar masu kaɗa ƙuri’a musulmai.

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare: INEC ta sanar da ranar zaben shugaban kasa da na gwamnoni a 2027

Source: Twitter
Tsohon hadimin shugaban kasar ya bayyana haka ne a wani sako da ya turawa hukumar INEC, wanda ya wallafa a shafinsa na X yau Juma'a.
Ranakun da ware na zaben 2027
INEC ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Tarayya ranar 20 ga Fabrairu, 2027, yayin da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi zai gudana ranar 6 ga Maris, 2027.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana ranakun a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja.
Abin da Bashir Ahmad ya hango a zabe
Da yake mayar da martani a shafinsa, Bashir Ahmad ya nuna damuwa cewa duka ranakun zaɓen sun faɗa ne a cikin watan Ramadan.
Ya rubuta cewa:
“Hukumar INEC, mun lura da wasu abubuwa bayan sanar da ranakun 20 ga Fabrairu da 6 ga Maris, 2027, a matsayin ranakun zaɓen Shugaban Ƙasa da Majalisar Tarayya, da kuma na gwamnoni da majalisun jihohi.
“Waɗannan ranaku sun faɗa ne cikin watan Ramadan, lokacin da Musulmi ke ware lokaci mai yawa domin azumi, ibada da zurfafa tunani na addini.”
2027: Matsalar da za a samu saboda azumi
Bashir Ahmad ya yi gargadin cewa gudanar da zaɓe a irin wannan lokaci na iya kawo ƙalubale ga dimbin al’umma.
“Idan manufar ita ce ƙarfafa jama’a su fito su kada kuri'a zaɓe, tsara irin wannan muhimmin abu a watan Ramadan na iya kawo cikas ga mafi yawan yan Najeriya."

Source: Facebook
Ya bayyana cewa a lokacin azumi, Musulmi kan rage shiga ayyuka masu wahala domin mayar da hankali kan ibada.
A ƙarshe, ya ce:
“Duba da yawan da Musulmi ke da shi a ƙasar nan, zai dace a sake duba jadawalin domin tabbatar da mutane sun bada hadin kai wajen fitowa da sauƙaƙa wa kowa.”
INEC ta fitar da jadawalin zaben 2027
A baya, an ji cewa Hukumar zaben Najeriya mai zaman janta watau INEC ta saki jadawalin babban zaben 2027 mai zuwa.
INEC ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin gudanar da zaben shekarar 2027 kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya dora mata.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a, 13 ga watan Fabrairu, 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
