Jam'iyyar NNPP Ta Kunnowa Kwankwaso Wata Wuta kan Zargin da Amurka Ke Yi Masa
- Tsagin jam'iyyar NNPP ya nesanta kansa daga zargin da wasu 'yan majalisar Amurka ke yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- NNPP ta bayyana cewa ba ta ji dadin mu'amalarta da Kwankwaso ba kafin daga bisani ta dauki matakin korarsa daga jam'iyyar
- Jam'iyyar ta bukaci hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro da su yi wasa da zargin da Amurka ke yi wa Kwankwaso
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ogun - Tsagin jam’iyyar NNPP ya yi magana kan yunkurin wasu 'yan majalisar Amurka na ganin an kakabawa Rabiu Musa Kwankwaso takunkumi.
NNPP ta bukaci hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da bincike cikin gaggawa kan zargin cewa kasar Amurka ta sanya sunan Sanata Rabiu Kwankwaso a matsayin mai tallafa wa ta’addanci.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar NNPP na kasa, Oginni Olaposi Sunday, ya sanya wa hannu, kuma ya aikawa jaridar Vanguard a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Jam'iyyar NNPP na son a binciki Kwankwaso
Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa kada a dauki wannan zargi da wasa, tana mai jaddada cewa tsaron kasa ya kamata ya zama gaba da duk wani ra’ayin siyasa.
“Babu wani mutum daya da ya fi kasa girma, musamman idan al’amuran da suka shafi tsaron kasa suka taso.”
- Oginni Olaposi Sunday
NNPP ta tuna alakarta da Kwankwaso
Jam’iyyar ta bayyana cewa mu’amalarta da Kwankwaso a cikin shekaru ukun da ya yi yana tare da NNPP ya tayar da damuwa game da halinsa da salon jagorancinsa.
“Mu’amalar mu da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a cikin shekaru uku da suka gabata ta nuna a fili cewa shi ba mutumin zaman lafiya ba ne, domin ya kawo rudani a cikin jam’iyyar siyasar da ta dade tana zaman lafiya na tsawon shekaru 22 kafin ya shiga cikinta."
- Oginni Olaposi Sunday
Zargin da NNPP ta ke yi wa Kwankwaso
Haka kuma, NNPP ta yi zargin cewa Kwankwaso ya haifar da rikicin cikin gida a jam’iyyar, ciki har da takaddama da wanda ya kafa ta, Dr. Boniface Aniebonam, wanda jam’iyyar ta ce shi ne ya ba shi dandalin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
"Abin takaici ne kwarai yadda aka zargi Sanata Kwankwaso da gallaza wa kowa da ya hadu da shi a NNPP, har ma da wanda ya kafa jam’iyyarmu wanda ya ba shi dandalin tsayawa takara a 2023 ba tare da ya biya ko sisin kwabo ba.”
- Oginni Olaposi Sunday
Jam’iyyar ta kuma yi nuni da hukunce-hukuncen kotunan sauraron korafe-korafen zabe a Kano bayan babban zaben 2023, inda ta yi ikirarin cewa wasu hujjoji na shari’a sun siffanta tafiyar Kwankwasiyya da wasu kalamai masu cike da cece-kuce.

Source: Facebook
Jam'iyyar NNPP ta raba gari da Kwankwaso
A cewar NNPP, shugabancin jam’iyyar ya dakatar da yarjejeniyar fahimtar juna da suka kulla da kungiyar Kwankwasiyya jim kadan bayan zaben 2023, sannan daga baya suka kori Kwankwaso saboda zargin ayyukan adawa da jam’iyya da kuma cin hanci da rashawa.
Jam’iyyar ta bukaci hukumomin kasar Amurka da gwamnatin tarayya da kada su danganta ta da duk wani zargi na ta’addanci da ake alakantawa da tsohon dan takarar shugaban kasar, tana mai cewa ya kamata a dauki kowane irin mataki a matsayin wani abu da ya shafe shi a kashin kansa.
Mataimakin Gwamnan Kano ya kare Kwankwaso
A wani labarin kuma, kun ji cewa Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya aika sako ga majalisar dokokin Amurka.
Aminu Abdulsalam Gwarzo ya bukaci majalisar dokokin Amurka da ta cire sunan Rabiu Musa Kwankwaso daga cikin jerin wadanda ake so a sanyawa takunkumi.
Ya bayyana cewa Kwankwaso ya dade yana adawa da tashe-tashen hankula, tsattsauran ra’ayi, da ta’addanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


