Yadda Ukraine Ta Kashe 'Yan Najeriya da Suka Shiga Sojan Rasha a Fagen Daga
- Ana cigaba da samun bayanai game da 'yan Najeriya da suka rasu bayan shiga soja a yakin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine
- Gwamnatin Ukraine ta fitar da sunayen wasu 'yan Najeriya da ta bayyana cewa ta ragargaje su sun mutu bayan wani farmaki da ta kai musu
- Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan jakadan Rasha a Najeriya ya fito karara ya karyata rahoton da ke cewa suna daukar 'yan kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ukaraine - Gwamnatin Ukraine ta ce ta gano wasu ‘yan Najeriya biyu da suka mutu yayin da suke fafatawa a bangaren Rasha a yaƙin da ke gudana tsakanin ƙasashen biyu.
Ukraine ta ce ‘yan Najeriyar sun shiga rundunar sojin Rasha ne a ƙarshen shekarar 2025 bayan sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ƙasar.

Source: Facebook
Rasha: Ukraine ta kashe 'yan Najeriya
A wata sanarwa da ta fitar a Facebook, hukumar leken asirin sojin Ukraine ta bayyana sunayen 'yan Najeriyan da Hamzat Kolawole da Mbah Udoka da ta ce an kashe su ne a yankin Luhansk da ke Gabashin Ukraine.
Sanarwar ta kara da zargin cewa babu ɗayansu da ya samu cikakken horon soja kafin a tura su fagen daga:
“Udoka bai samu wani horo ko kaɗan ba — kwana biyar kacal bayan daukarsa, a ranar 3 ga Oktoba, aka sanya shi cikin wata runduna tare da tura shi zuwa yankunan Ukraine.
"Babu wasu bayanan horo da aka adana na Kolawole; amma akwai yiwuwar shi ma bai samu horon soja ba. Matarsa da ‘ya’yansa uku suna nan a Najeriya,”
An ce su biyun sun mutu ne a watan Nuwamban 2025 yayin wani yunƙuri na kai hari kan sansanonin sojojin Ukraine a yankin Luhansk.
“Ba su samu damar shiga musayar wuta ba — an hallaka su ne ta hanyar hari da jirgin sama mara matuƙi,”
- Inji hukumar leken asirin sojin Ukraine
Tun daga shekarar 2025, rahotanni na nuna ƙaruwa a lokutan da ake ɗaukar ‘yan Najeriya da sauran ‘yan Afirka domin shiga yaƙi a gefen sojojin Rasha a Ukraine.

Source: Getty Images
An kashe sojoji miliyan 2 a yakin Rasha-Ukraine
Wani rahoton jaridar New York Times ya nuna cewa kimanin sojoji miliyan biyu daga Rasha da Ukraine sun mutu a kusan shekaru huɗu na yaƙin.
Bincike daban-daban sun nuna lokuta da ake zargin an ja hankalin wasu da alkawuran samar da aiki, albashi mai tsoka ko damar karatu, amma daga baya suka tsinci kansu a fagen daga.
Sojojin haya: Rasha ta karyata daukar 'yan Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin Rasha ta karyata rahoton da ke cewa tana daukar sojoji daga Najeriya da wasu kasashen Afrika ba bisa ka'ida ba.
Jakadan kasar Rasha a Najeriya, Andrey Podyolyshev ne ya bayyana haka, inda ya ce ba su da wani labarin da ya ke tabbatar da zargin.
Andrey Podyolyshev ya kara da cewa a shirye gwamnatin Rasha ta ke ta kaddamar da cikakken bincike idan aka gabatar mata da hujjoji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

