An Zo wajen: Gwamnatin Abba Ta Yi Magana kan Batun Hana Kwankwaso zuwa Kano
- Babban jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya yi zargin cewa ana kokarin hana Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shigowa jihar Kano saboda dalilai na siyasa
- Gwamnatin jihar Kano ta fito ta yi martani kan zargin na Buba Galadima, inda ta bayyana yadda abubuwa suke
- Ta bayyana cewa ko kadan ba ta taba yunkurin rubuta wata takarda ga gwamnatin tarayya ba domin hana Kwankwaso shigowa Kano
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan zargin da ke cewa tana shirin hana Rabiu Musa Kwankwaso cikinta.
Gwamnatin ta musanta ikirarin da ake yi na cewa tana kokarin hana Kwankwaso shiga jihar, inda ta siffanta zargin a matsayin ƙarya kuma kokari ne na yaudarar jama’a da gangan.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Waiya, ya fitar a ranar Alhamis, 12 ga watan Fabrairun 2026.
Buba Galadima ya jefi gwamnatin Kano da zargi
Wannan musantawar ta biyo bayan wasu kalaman da aka ce sun fito ne daga bakin makusancin Kwankwaso, Buba Galadima.
Buba Galadima dai ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Abba Yusuf ta rubuta wa gwamnatin tarayya takarda domin ta dakatar da Kwankwaso daga ziyartar Kano.
Wani martani gwamnatin Kano ta yi?
Kwamishinan yada labarin ya yi watsi da zargin a matsayin mara tushe ballantana makama, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da hakan.
“Gwamnatin jihar Kano ta lura cikin damuwa game da zargi marar tushe da Alhaji Buba Galadima ya yi, na cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rubuta wa gwamnatin tarayya takardar neman hana Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shigowa jihar Kano.”
“Muna son bayyana wa duniya dalla-dalla cewa wannan zargi karya ne kuma wani yunƙuri ne da gangan domin yaudarar jama’a da kuma haifar da zaman ɗar-ɗar na siyasa da ba a buƙatarsa a jihar."
- Ibrahim Abdullahi Waiya
Ba a yi yunkurin hana Kwankwaso zuwa Kano ba
Gwamnatin ta kara jaddada cewa ba a taɓa yin wata rubutacciyar takarda kan irin hakan ga kowace hukuma ba, tana mai cewa ikirarin bai da tushe ballantana makama.
“Babu wani lokaci da gwamnatin jihar Kano ta rubuta wa Gwamnatin Tarayya ko wata hukuma da nufin hana Sanata Kwankwaso, ko wani ɗan Najeriya, shiga Jihar Kano."
"Irin wannan ikirari yana nan ne kawai a cikin tunanin waɗanda suka ƙirƙire shi, don haka ya kamata a kalle shi da idon raini domin abin da ya dace da shi ke nan."
- Ibrahim Abdullahi Waiya

Source: Facebook
Gwamnatin Kano na kiyaye 'yancin kowa
A cewar gwamnatin, Kano tana ci gaba da kasancewa mai kiyaye ’yancin da kundin tsarin mulki ya bayar da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar.
“Kano tana ci gaba da kasancewa jiha mai zaman lafiya da bin doka, inda ake girmama tare da kare haƙƙoƙin kowane ɗan ƙasa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, tare da ’yancin yin zirga-zirga da ƙungiyanci.”
“Gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta fi mayar da hankali ne kan shugabanci, gudanar da ayyuka, da jin daɗin jama’a, ba wai kan abubuwan shagala na siyasa marasa amfani ba."
- Ibrahim Abdullahi Waiya
Kwankwasiyya ta aika sako kan Kwankwaso
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Kwankwasiyya ta yi martani kan zargin da ake yi wa Rabiu Musa Kwankwaso na tauye 'yancin hakkin addini.
Kungiyar siyasar ta yi kira ga majalisar dokokin Amurka ta cire sunan Kwankwaso daga cikin jerin wadanda ake zargi da tauye hakkin addini.
Kwankwasiyya ta bayyana saka sunan tsohon gwamnan Kano a cikin kudirin dokar a matsayin kage marar tushe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


