Lamari Ya Girma: Bayan Ganawa da Tinubu, Gwamna Ya Kori Duka 'Yan Majalisar Zartawa

Lamari Ya Girma: Bayan Ganawa da Tinubu, Gwamna Ya Kori Duka 'Yan Majalisar Zartawa

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya rusa majalisar zartarwar jihar tare da sallamar dukkan kwamishinonin gwamnati

  • An umarci mambobin majalisar da su mika ragamar aiki ga manyan sakatarorin ko manyan jami’an ma’aikatunsu nan take
  • Wannan mataki ya zo ne kwanaki biyu bayan ganawar sulhu da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta domin warware rikicin siyasar jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Gwamnan Rivers, Sir Siminalayi Fubara, ya sanar da rusa Majalisar Zartarwar Jihar ba tare da bata lokaci ba.

Gwamna Fubara wanda ya shiga ofis a 2023 ya gode wa mambobin majalisar bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar.

Fubara ya kori kwamishinoni da hadimansa a Rivers
Gwamna Siminalayi Fubara. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labaransa, Onwuka Nzeshi, ya fitar wanda Vanguard ta samu.

Wainar da aka toya a ganawar Tinubu, Fubara

Kara karanta wannan

Gwamnan Gombe ya hada kai da Tunisia, ya fadi harkokin da za su yi tare

Matakin rushe majalisar ya zo ne sa’o’i 48 bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya tabbatar da cewa ana kokarin sasanta rikicin siyasa da ya dade yana faruwa a jihar.

Ministan ya ce Bola Ahmed Tinubu ya gana da manyan ‘yan siyasar Rivers, ciki har da Gwamna Fubara da wanda ya gada, domin rage zafin rikicin da ya dabaibaye jihar mai arzikin man fetur.

An gudanar da taron ne a Fadar Shugaban Kasa a Abuja a bayan fage, inda wasu manyan shugabannin jihar ma suka halarta, a wani sabon yunkuri na samar da zaman lafiya a jihar.

An gana tsakanin Wike, Fubara da Tinubu
Shugaba Bola Tinubu, Nyesom Wike da Siminalayi Fubara. Hoto: Bayo Onanuga, Nyesom Wike.
Source: Twitter

Umarnin da Fubara ya ba korarrun mukarrabansa

Gwamnan ya umarci dukkan kwamishinoni da masu ba shi shawara na musamman da su mika ragamar aiki nan take, cewar Punch.

Sanarwar ta ce:

“Mai Girma Gwamnan Jihar Rivers, Sir Siminalayi Fubara, GSSRS, ya rusa Majalisar Zartarwar Jihar."

Sanarwar ta kara da cewa gwamnan ya umurci dukkan kwamishinoni da masu ba shi shawara da su mika aiki ga manyan sakatarori ko manyan jami’ai a ma’aikatunsu ba tare da bata lokaci ba.

Kara karanta wannan

IFAD: Ministan Tinubu ya samu gagarumar nasara, an ba shi babban mukami a duniya

Godiyar Fubara zuwa ga tsofaffin kwamishinoninsa

Haka kuma, gwamnan ya bayyana matukar godiyarsa ga tsofaffin mambobin majalisar, yana musu fatan alheri a dukkan abubuwan da suka sanya a gaba.

“Don haka Mai Girma Gwamnan ya umurci dukkan Kwamishinoni da Masu ba shi Shawara na Musamman da su mika ragamar aiki ga manyan sakatarori ko manyan jami’ai mafi girma a ma’aikatunsu nan take.
“Mai Girma Gwamnan ya kuma bayyana matukar godiyarsa ga mambobin Majalisar Zartarwa da suka kammala wa’adinsu, yana musu fatan alheri a dukkan kokarinsu na gaba.”

'Dalilin hana Wike shiga filin wasa' - Gwamnatin Rivers

An ji cewa Gwamnatin Rivers ta ce ba ta hana Nyesom Wike shiga filin wasa ba, ta bayyana cewa babu wata takardar neman izini daga gare su.

An ce ana ci gaba da gyare-gyare a filin wasan kuma ba shi da aminci ga taron jama’a, lamarin da ya sa aka hana duk wani taro.

Gwamna Simi Fubara ya jaddada goyon bayansa ga Bola Tinubu, yana cewa gwamnatin Rivers na sahun gaba wajen tallafa wa sake zaɓensa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.