Bayan Abin da Ya Faru a Filin Jirgi, El Rufai Zai Gurfana a Gaban Hukumar EFCC
- Lauyan Malam Nasiru El-Rufai ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan zai amsa gayyatar EFCC a ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu, 2026
- Barista Ubong Esop Akpan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan yunkurin da jami'an tsaro suka yi na kama El-Rufai a filin jirgin sama a Abuja
- Ya ce abin da jami'an tsaron suka yi ya saba wa tanadin kundin tsarin mulki, yana mai cewa sun sanar da EFCC halin da ake ciki tun farko
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, zai gurfana a gaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Litinin mai zuwa.
Lauyansa, Ubong Esop Akpan, ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan yunƙurin kama Malam El-Rufai a filin jirgin saman Abuja.

Source: Facebook
El-Rufai ya wallafa cikakkiyar sanarwar da lauyan ya fitar bayan abin da ya faru a filin jirgin sama a shafinsa na Facebook da yammacin yau Alhamis.
Yadda aka yi yunkurin kama Nasir El-Rufai
Ya ce jami’an tsaro sun tunkari El-Rufai ne da yammacin Alhamis bayan ya isa Abuja ta jirgin Egypt Air mai lamba MS 877 daga birnin Cairo na ƙasar Masar.
Akpan ya bayyana yunƙurin kama tsohon gwamnan a matsayin keta hakkin dan Adam da kundin tsarin mulki ya tanada, da kuma wuce gona da iri.
“Gayyatar da EFCC ta aike wa Malam El-Rufai ta iso ne yayin da yake ƙasar waje, wanda hakan ya sa ba zai yiwu a buƙaci ya amsa gayyatar nan take ba.
"Ba zai yiwu a yi tsammanin mutumin da ke wajen ƙasa ya kai kansa ofishin EFCC ba, ya riga ya yi tafiya, don haka ya kamata a masa adalci,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Yadda fasinjoji suka hana jami'an tsaro kama El Rufai a filin jirgin sama
El-Rufai zai gurfana a gaban EFCC
Lauyan ya ce tun watan Disamba na 2025 suka rubuta wa EFCC wasika don tabbatar da cewa El-Rufai zai amsa gayyatar da zarar ya dawo ƙasa.
Ya ƙara da cewa a ranar Laraba sun sake sanar da hukumar cewa tsohon gwamnan zai je ofishinsu da kansa da misalin ƙarfe 10:00 na safe ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026.
“Yunƙurin kama shi duk da wannan wasika da muka tura na nuna son rai da kuma tauye tsarin doka,” in ji Akpan.

Source: Twitter
Ya kuma ce babu wani dalili na doka da zai ba da hujjar yunƙurin kama shi, yana mai cewa hakan ya saba wa muhimman tanade-tanaden kundin tsarin mulki da ke kare ‘yancin dan Adam.
Akpan ya ce duk da sun samu bayanan sirri cewa ana shirin kama shi, El-Rufai ya dawo ƙasar bayan jinya da hutu a waje, yana mai bayyana shirinsa na fuskantar duk wani bincike na doka.

Kara karanta wannan
Jami'an tsaro sun ga takansu da suka yi yunkurin kama El Rufai a filin jirgin sama
El-Rufai ya yi hasashen za a kama shi
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i ya yi ikirarin cewa zai iya shiga hannun hukumomin Najeriya nan ba da jimawa ba.
El-Rufai fadi haka ne saboda yadda aka kama wasu daga cikin wadanda suka yi aiki da shi a lokacin da ya ke gwamna na tsawon shekaru takwas a Kaduna.
Tsohon Ministan harkokin Abujan ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke kara zafi yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Asali: Legit.ng
