Yunkurin Kama El Rufai, Lauyoyi Sun Zayyana Dokoki 5 da Jami'an Tsaro Suka Take

Yunkurin Kama El Rufai, Lauyoyi Sun Zayyana Dokoki 5 da Jami'an Tsaro Suka Take

  • Lauyan Nasir El-Rufai ya soki jami'an tsaro kan yunkurin kama tsohon gwamnan a filin jirgin Abuja ba tare da takardar izini ba
  • Ubong Akpan ya tabbatar da cewa El-Rufai zai bayyana a ofishin EFCC ranar Litinin domin amsa gayyata kamar yadda aka tsara
  • Sanarwar ta zargi jami'an tsaro da 'sace' fasfon El-Rufai wanda hakan ya saba wa wasu sassan kundin tsarin mulkin Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Lauyan Nasir El-Rufai, Ubong Akpan, ya zargi jami'an tsaron Najeriya da yunkurin kama tsohon gwamnan ba tare da bin ka'idojin shari'a ba.

A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Alhamis, 12 ga Fabrairu, 2026, Akpan ya bayyana cewa jami'an sun far wa El-Rufai ne bayan ya dawo daga Cairo.

Lauyoyin El-Rufai sun fadi sashen kundin tsarin mulki da jami'an tsaro suka taka a yunkurin kama shi.
Malam Nasir El-Rufai ya na magana da jami'an tsaron da suka yi yunkurin kama shi a Abuja. Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Facebook

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya wallafa wannan sanarwar a shafinsa na Facebook, jim kadan bayan barin filin jirgin Abuja.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda fasinjoji suka hana jami'an tsaro kama El Rufai a filin jirgin sama

Rashin amsa gayyatar EFCC da wuri

Lauyan ya bayyana wannan mataki a matsayin taka hakkin dan adam da kuma yin gaban-kai wanda ya saba wa tsarin mulkin kasar Najeriya.

A cewar lauyan, hukumar EFCC ta aika da takardar gayyata ne tun El-Rufai yana kasar waje, wanda hakan ya sa ba zai yiwu ya amsa ba.

“Mun sanar da EFCC tun watan Disambar 2025 cewa zai bayyana a ofishinsu da zarar ya dawo Najeriya, kuma jiya mun sake tabbatar musu da hakan.”

- Ubong Akpan.

Lauyan ya jaddada cewa El-Rufai ya riga ya tsayar da ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, domin ya mika kansa ga EFCC da misalin karfe 10:00 na safe.

"Saboda haka, yunkurin kama shi kafin wannan lokacin ya nuna rashin bin tsarin aiki da kuma nuna iko ba tare da bin ka'ida ba," a cewar lauyan.

Batun kwace fasfon El-Rufai a filin jirgi

Akpan ya zargi jami’an tsaro da kwace fasfon tsohon gwamnan ta karfin tsiya, inda ya bayyana hakan a matsayin sata da wakilan gwamnati suka aikata.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun ga takansu da suka yi yunkurin kama El Rufai a filin jirgin sama

A cewar lauyan:

“Jami’an sun kwace fasfon sa ba tare da nuna takardar izini ko umarni daga kotu ba, wanda hakan ya saba wa sashi na arba’in da hudu.”

Ya kuma yaba wa talakawan Najeriya da suka nuna kin amincewa a filin jirgin, inda suka tilasta wa jami’an tsaron bin tsarin dokokin kasa, in ji rahoton Punch.

Lauyan ya ce abin kunya ne yadda ‘yan kasa ne suka rika tunatar da jami’an tsaro muhimmancin bin kundin tsarin mulki yayin gudanar da ayyukansu.

Lauyoyi za su dauki matakin shari'a kan jami'an tsaron da suka yi yunkurin kama El-Rufai.
Malam Nasir El-Rufai yana zaune a filin jirgin Abuja lokacin da aka ce an yi yunkurin kama shi. Hoto: @MuyiwaAdekeye
Source: Twitter

Sassan kundin tsarin mulki da aka take

Ubong Akpan ya lissafo sassan kundin tsarin mulkin Najeriya da jami'an tsaron suka taka yayin dambarwar da ta faru a filin jirgin saman Abuja:

  • Sashi na 35 (Haƙƙin samun ƴanci): Wannan sashi ya tanadi cewa dole ne kamun ya kasance mai tushe kuma bisa ƙa'idodin shari'a da kotu ta yarda da su.
  • Sashi na 36 (Haƙƙin samun adalci): Wannan yana kare ɗan ƙasa daga duk wani mataki na hukuma wanda zai iya kawo cikas ga tsarin shari'ar da ake gudanarwa.
  • Sashi na 34 (Haƙƙin mutuncin ɗan adam): Wannan sashi yana kare ɗan ƙasa daga cin mutunci ko wulaƙanci yayin da jami'an tsaro suke ƙoƙarin kama shi.
  • Sashi na 41 (Haƙƙin walwala da zirga-zirga): Wannan sashi ya tabbatar da cewa ɗan ƙasa yana da haƙƙin shiga ƙasarsa ba tare da wani shamaki na kama-karya ba.
  • Sashi na 44 (Haƙƙin mallakar dukiya): Wannan sashi ya haramta wa jami'an gwamnati ƙwace fasfo ko wata dukiya ta ɗan ƙasa ba tare da izinin doka ko kotu ba.

Kara karanta wannan

El Rufai zai mika kansa ga hukumar EFCC, ya sanya ranar da zai dawo Najeriya

Barazanar da lauyoyin El-Rufai suka yi

Lauyan tsohon gwamnan ya bayyana cewa ƙwace fasfon El-Rufai da jami'an suka yi ba komai ba ne face "sata" duba da cewa ba su nuna takardar izinin yin haka ba.

Daga ƙarshe, ya yi barazanar ɗaukar matakin shari'a a kan dukkan jami'an da suka sa hannu a wannan yunƙuri na kama tsohon gwamnan ba tare da izini ba.

Fasinjoji sun hana a kama El-Rufai

Tun da fari, mun ruwaito cewa, jami'an tsaro sun yi yunkurin kama tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai a filin jirgin Abuja yau bayan ya dawo daga Cairo.

Wani bidiyo ya nuna yadda fasinjoji da magoya baya suka hana jami'an tsaron tafiya da tsohon gwamnan, amma duk da haka aka kwace fasfonsa.

Nasir El-Rufai ya kalubalanci jami'an tsaron da su mika masa takardar gayyata maimakon su yi kokarin kama shi ta karfin tsiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com