Bayan Zargin Kwankwaso, Amurka Za Ta Mamaye Wani Ɓangaren Tsaron Najeriya
- Amurka ta gabatar da kudiri a Majalisar Wakilai domin hada kai da Najeriya wajen dakile hakar ma’adinan China ba bisa ka’ida ba
- Masu gabatar da kudirin sun zargi wasu ‘yan China da biyan kudin kariya ga Fulani, lamarin da ke kara rura wutar rashin tsaro
- Kudirin ya bukaci a tantance wasu kungiyoyin Fulani a matsayin ‘yan ta’adda, tare da karfafa hadin gwiwa kan ‘yancin addini da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - An kawo sabon kudiri wanda aka gabatar a Majalisar Wakilan Amurka game da rashin tsaro a Najeriya.
Kudirin ya bukaci Sakataren Harkokin Waje ya hada kai da gwamnatin Najeriya domin dakile hakar ma’adinan China ba bisa ka’ida ba da kuma tada rigima na wasu Fulani.

Source: Facebook
Sabon kudiri da Majalisar Amurka ta kawo

Kara karanta wannan
Da mamaki: Bulama ya ga kuskuren amurka kan zargin kwankwaso da matsawa kiristoci
An gabatar da kudirin mai taken 'Nigeria Religious Freedom and Accountability Act of 2026' domin hada kai da samar da yancin addini, cewar rahoton TheCable.
Majiyoyi sun ce an gabatar da kudirin wanda ‘yan majalisar Republican biyar suka dauki nauyi, ciki har da Chris Smith, Riley Moore, Brian Mast, Mario Diaz-Balart da Bill Huizenga.
Masu daukar nauyin kudirin sun ce hakar ma’adinan China ba bisa ka’ida ba ya hada da “biyan kudin kariya ga Fulani,” abin da suka ce na taimakawa wajen daukar nauyin hare-hare da rashin tsaro a yankin.
Sashe na 10 da 11 na kudirin sun bukaci Sakataren Harkokin Waje ya bai wa Najeriya tallafin fasaha domin ragewa da kuma kawo karshen tashin hankali daga Fulani, ciki har da shirye-shiryen kwace makamai da hadin gwiwar yaki da ta’addanci.
Haka kuma kudirin ya umurci gwamnatin Amurka ta hada kai da kasashe kamar Faransa, Hungary da Birtaniya domin bunkasa ‘yancin addini da zaman lafiya a Najeriya.

Source: Getty Images
Abin da kudirin ke bukata daga ministan tsaro
Kudirin ya kuma dora wa Sakataren Harkokin Waje alhakin tantance ko wasu kungiyoyin Fulani sun cancanci a ayyana su a matsayin “Kungiyoyin Ta’addanci.”
Wannan kudiri ya biyo bayan rahoton wanda ya zargi wasu ‘yan China da ke hakar ma’adanai a Zamfara da Arewa maso Yamma da bai wa kungiyoyin masu dauke da makamai kudade domin kare ayyukansu.
Rahoton ya nuna cewa wadannan kudade da hanyoyin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba na iya tallafawa ayyukan ta’addanci a Najeriya, wacce ita ce mafi girman tattalin arziki a Afirka, cewar TVC News.
Kudirin ya jawo muhawara kan yiwuwar tsoma bakin kasashen waje a harkokin tsaro da ma’adinai na Najeriya, inda wasu masana ke gargadi.
Fulani sun magantu kan takunkumin Amurka
Kun ji cewa Kungiyar Fulani makiyaya ta MACBAN ta ce ta yi mamakin yadda Majalisar dokokin Amurka ke shirin ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci.
Shugaban ƙungiyar, Baba Othman, ya bayyana matakin a matsayin rashin adalci da zai iya bata sunan ƙungiyar a Najeriya da duniya baki daya.
Hakan na zuwa ne bayan 'yan majalisar sun ba da shawarar ƙaƙaba takunkumi kan kungiyar da wasu mutane bisa zargin take hakkin Kiristoci.
Asali: Legit.ng
