Abubuwan da Aka Nemi Musulmi Su Kiyaye yayin da Ake Shirin Fara Azumin Ramadan
Kwara, Nigeria - Malamai da shugabannin addini sun yi kira ga Musulmi da su tsarkake zukatansu tare da nesanta kansu daga munanan ɗabi’u yayin da watan Ramadan mai alfarma ke ƙaratowa.
An yi wannan kira ne a wajen Taron shirye-shiryen Ramadan na shekara-shekara wanda ƙungiyoyin Musulunci guda bakwai a Jihar Kwara suka shirya.

Source: Getty Images
Ramadan wata makaranta ce ta tarbiyya
Daily Trust ta ce a cikin muhimmin jawabin da ya gabatar, Associate Prof. Hamza AbdulRaheem na Jami’ar Al-Hikmah ya bayyana Ramadan a matsayin wata ibada mai tsarki da ke koyar da ladabi, haƙuri da ibada ga muminai.
Ya ce:
“Watan Ramadan wata ibada ce ta azumi ga Musulmi. Lokaci ne da muminai ke koyon ainihin ma’anar ladabi, haƙuri da sadaukarwa ga Allah.”
Ya kuma kawo hadisin Manzon Allah (SAW) cewa:
“Duk wanda ya yi azumin Ramadan da imani da kyakkyawar niyya domin neman yardar Allah, za a gafarta masa zunubansa.”

Kara karanta wannan
Bayan turo sojoji, Amurka za ta kafa 'tashar jiragen yaki' a a jihar Arewacin Najeriya
Gargadi kan amfani da kafafen sada zumunta
Sai dai malamin ya yi gargaɗi kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta, musamman a watan Ramadan.
Ya ce kafafen sada zumunta na iya zama alheri ko sharri gwargwadon yadda ake amfani da su, kamar yadda Guardian ta rahoto.
A gefe mai kyau, ya ce ana iya amfani da su wajen sauraron karatun Alƙur’ani, wa’azi da darussan addini da ke ƙarfafa imani.
Amma ya yi kashedi cewa wasu na azumi amma suna aikata laifuffuka a yanar gizo kamar kallon abubuwan batsa, wanda hakan na iya rage ko lalata ladan azuminsu.
Muhimmancin Zakka da Waqafi
A nasa jawabin, Injiniya Ariyo Bashir Olalekan, Mai Kula da Asusun Zakka da Sadaka a jihar kuma Shugaban Kwamitin Shirya Taron, ya yi bayani kan muhimmancin Zakka da Waqafi da alaƙarsu da watan Ramadan.
Ya bayyana cewa Zakka ɗaya ce daga cikin ginshiƙan Musulunci biyar, kuma hakki ne da Allah ya wajabta wa masu hali domin tallafa wa marasa ƙarfi.
“Zakka ba sadaka ce ta son rai ba, hakki ne da Allah ya ɗora wa masu arziki su bai wa talakawa,” in ji shi.
Ya bayyana cewa duk Musulmin da dukiyarsa ta kai ƙimar Nisabi kuma ta zauna a hannunsa tsawon shekara ɗaya ta kalandar Musulunci, wajibi ne ya fitar da kashi 2.5 cikin 100 na dukiyarsa a matsayin Zakka.
Ya kuma bayyana Waqafi a matsayin sadaka da ake ware dukiya ko fili domin amfanin al’umma saboda Allah, inda amfanin da ake samu daga gare ta ke tallafa wa marayu, zawarawa, marasa lafiya da sauran masu buƙata.

Source: Getty Images
Ladan ibada a Ramadan ya ninka
Olalekan ya ƙara da cewa ibada a watan Ramadan na da lada mai yawa domin Allah SWT na nunnunka wa bayinsa lada idan suka yi ibada a watan azumi.
"Idan kuma aka yi farilla kamar Zakka a Ramadan, ladan na ƙaruwa matuƙa, muddin niyya ta kasance tsarkakakkiya,” in ji shi.
A ƙarshe, ya buƙaci Musulmi su rungumi Zakka da Waqafi a matsayin hanyoyi na tabbatar da adalci da tausayi a cikin al’umma, musamman a wannan lokaci mai alfarma.
Saudiyya ta yi sanarwar duban watan Ramadan
A wani labarin, kun ji cewa kasar Saudiyya ta bukaci musulmi da su fara duba jinjirin watan Ramadan a yammacin ranar Talata, 17 ga watan Fabrairu, 2026.
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da shafin watsa labaran masallatai biyu masu alfarma na Inside the Haramain ya fitar.
Idan har aka ga watan a wannan rana, kuma kwamitin koli na ganin watan ya tabbatar da hakan, to Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026 za ta zama 1 ga watan Ramadan, 1447AH a Saudiyya.
Asali: Legit.ng

