Gwamna na Tsaka Mai Wuya game da Maye Gurbin Mataimakinsa da Ya Mutu
- Rikicin siyasa ya kara kamari a Bayelsa yayin da ake tattaunawa kan wanda zai maye gurbin marigayi mataimakin gwamna
- Wasu sun bukaci a bar Sagbama ta kammala wa’adin, yayin da wasu ke cewa tsarin rabon mukamai ne ya kamata a bi
- Tsohon gwamna Seriake Dickson ya ce ikon nada mataimaki yana hannun Gwamna Diri kadai, yana mai gargadin a guji matsa masa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yenagoa, Bayelsa - Ana ci gaba da tada jijiyoyin wuya da tuntuba a jihar Bayelsa kan wanda zai gaji marigayi mataimakin gwamna.
Har yanzu ba a maye gurbin marigayi Lawrence Ewhrudjakpo, bayan rasuwarsa a karshen shekarar bara.

Source: Facebook
Tun kafin a yi jana’izarsa, an fara neman goyon baya da tattaunawa, musamman bayan ya ki bin Gwamna Douye Diri komawa jam’iyyar APC daga PDP, cewar Punch.
Yaushe mataimakin gwamnan Bayelsa ya tafi?
Marigayin ya rasu ne ranar 11 ga Disamba, 2025, yana da shekaru 60, bayan ya fadi a ofishinsa da ke Yenagoa.
An garzaya da shi zuwa Asibitin Tarayya da ke Yenagoa inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa bayan kokarin ceto rayuwarsa.
Rasuwarsa ta jawo muhawara kan ko Sagbama, inda ya fito, ya kamata ta samar da wanda zai maye gurbinsa.
An fara neman kujerar marigayin
Wasu masu ruwa da tsaki sun ce adalci ya bukaci a bar Sagbama ta kammala wa’adin kujerar mataimakin gwamna.
Sai dai wasu sun ce ya kamata a bi tsarin rabon mukamai a Bayelsa ta Yamma don kauce wa rikitar da daidaiton siyasa.
A kundin tsarin mulki, gwamna ne ke da ikon nada sabon mataimaki, amma sai majalisar dokoki ta amince.
Daga cikin sunayen da ake ambato akwai Dr Peter Akpe, Christopher Ewhrudjakpo, Abraham Ingobere da Dr Dennis Otiotio.

Source: Twitter
Tsohon gwamna ya soki masu hadamar kujerar

Kara karanta wannan
'Ba a sarki 2,' Tsohon kwamishina ya fadi dalilin batawar Abba da Kwankwaso a Kano
Tsohon gwamna Seriake Dickson ya soki yadda ake ta neman mukamin tun kafin a yi jana’izar marigayin.
Ya ce:
"Babu jayayya kan wanda zai nada mataimaki, ikon yana hannun gwamna kamar yadda doka ta tanada.”
Ya kara da cewa bai taba matsa wa Gwamna Diri lamba ba cikin shekaru shida da suka gabata, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Shugaban kungiyar 'Civil Liberties Organisation' a Bayelsa, David West, ya ce kujerar ta dace ta ci gaba da kasancewa a Sagbama.
Ya bayyana cewa tsarin rabon mukamai da aka amince da shi tun farko ya kamata a kiyaye shi.
West ya kuma ce jinkirin nada sabon mataimaki saba wa tsarin mulki ne, duk da ana cikin alhinin rasuwar marigayin.
An rasa rai yayin jana'izar mataimakin gwamna
Mun ba ku labarin cewa a ranar Juma'a, 30 ga Janairu, 2026 aka yi jana'izar mataimakin gwamnan Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, wanda ya rasu a watan Disamba, 2025.
Rahotanni sun nuna cewa mutum biyu sun mutu a hanyarsu ta zuwa wannan jana'iza a garin garin Ofoni da ke Karamar Hukumar Sagbama, a jihar Bayelsa.
Hukumar 'yan sanda da gwamnatin jihar Bayelsa sun tabbatar da aukuwar hatsarin, sun ce ana ci gaba da tantance wadanda mummunan lamarin ya shafa.
Asali: Legit.ng
