El Rufai Ya Yi Tone Tone, Ya Fallasa Shirin Gwamnatin Tinubu Na Murde Zaben 2027

El Rufai Ya Yi Tone Tone, Ya Fallasa Shirin Gwamnatin Tinubu Na Murde Zaben 2027

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi zarge-zarge kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu dangane da zaben 2027
  • El-Rufai ya nuna cewa gwamnatin Tinubu na son yin amfani da kafar da aka ba da a dokar zabe wajen tafka magudi
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa idan ana so, tabbas za a iya tura sakamakon zabe ta intanet daga ko'ina a Najeriya

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana kan dokar zaben da majalisa ta amince da ita.

El-Rufai ya yi zargin cewa gwamnatin Bola Tinubu na iya amfani da kafar da aka ba da a dokar zabe wajen tafka magudi a zaben shekarar 2027.

Nasir El-Rufai ya yi zarge-zarge kan gwamnatin Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu da Nasir El-Rufai Hoto: Kashim Shettima, Nasir El-Rufai
Source: Facebook

Tsohon gwamnan na Kaduna ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da DCL Hausa wadda aka sanya a shafin Facebook a ranar Laraba, 11 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

El Rufai zai mika kansa ga hukumar EFCC, ya sanya ranar da zai dawo Najeriya

Wane zargi El-Rufai ya yi kan gwamnatin Tinubu?

Ya bayyana cewa damar da aka ba da ta rubuta sakamakon zabe a inda babu intanet, ya ba da kafar da za a iya yin magudi kafin zuwa cibiyoyin tattara sakamako.

El-Rufai ya zargi gwamnatin da neman a bar kafar saboda ta samu damar yin magudin zabe.

"Gwamnatin Tinubu ba su tsoron Allah, ko shaidan ma ba su tsoron shi don tare suke. Za su yi kokarin bata zabe."
"Za ta yi kokarin haka, ai azzalumar gwamnati ce. Sun san ba za su ci zabe ba, sun sani sarai. Sun san inda zabe za a yi na Fisabilillahi wallahi ba za su ci ba."
"Saboda haka ba su da wata hanya sai dai su yi cuta. Sai dai su yi amfani da karfinsu na gwamnati su ce a rufe intanet a ranar zabe ko wani abun."
"Akwai Starlink ta Elok Musk, wanda kowane bangare na Najeriya ana samun Starlink. Indai ana so a yi, ana so a yi gaskiya, INEC sai ta yi aiki da Starlink ba ma sai ta dogara da kamfanonin sadarwa na Najeriya ba."

Kara karanta wannan

Nasir El Rufa'i ya fito ya yi magana daga kasar waje kan barazanar cafke shi

"Za ta iya yin kwangila da Starlink wadanda a Amurka suke, kowace mazaba a Najeriya za a iya samun Starlink."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya yi magana kan dokar zabe
Nasir El-Rufai a wajen taron jam'iyyar ADC Hoto: @elrufai
Source: Twitter

El-Rufai ya yi watsi da rashin intanet

El-Rufai ya yi watsi da ikirarin cewa wasu kauyukan ba su da intanet a Najeriya.

"Na ji wani sanata Orji Kalu wanda shi daman tsohon makaryaci ne yana cewa kauyen shi babu intanet. Abin kunya ne wanda ya yi gwamna shekara takwas, ya yi sanata shekara goma sha kuma wai har yanzu kauyen shi babu intanet, kuma na tabbata karya yake yi."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai zai mika kansa ga EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sanya lokacin dawowa gida Najeriya.

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya ce zai dawo gida Najeriya domin amsa kiran hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.

Nasir El-Rufai ya sanar da hukumar EFCC cewa zai bayyana a ofishinsu ranar Litinin, 16 ga Fabrairun 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng